Daga Susan Mwongeli
Kamar yadda mawakiyar Amurka kuma mai fafutuka ta bayyana karara. "tarihi, duk da zafin da yake da shi, ba za a iya kashe shi ba, amma idan aka tunkare shi da karfin zuciya, za a iya raya shi."
A wajen Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, kasa ta biyu mafi girman kasa a Afirka, bikin murnar cika shekara 64 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Belgium, ya zama lokaci na waiwaye da tuna baya.
Shekaru 63 kenan da 'yan a waren Kongo da Belgium da Amurka ke goya wa baya suka aikata kisan gilla ga zababben Firaminista na farko a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Patrice Lumumba.
Shekaru da dama bayan mutuwar Lumumba, a lokacin yana gaf da cika shekaru 36, har yanzu kasarsa na fama da dimbin matsalolin d aya kudiri aniyar kawarwa - katsalandan din kasashen waje, rikicin masu dauke da makamai, rashin zmaan lafiyar siyasa, mummunan jagoranci da talauci d aya zama gama-gari.
Da a ce Lumumba ya rayu, da tuni DRC ta dauki layi na daban da zai kai ta ga cigaban kasa.
Kasar da ke a dauke da kogunan Kongo, na da dimbin albarkatun kasa d agandun daji da ke daya daga cikin mafi girma a duniya.
A yayinda jama'ar Kongo miliyan 105 suke cikin talauci, duk da dimbin arzikin da suke da shi, sai kasashen yamma ne ke amfana da arzikin ta hanyar goyon bayan gurbatattun gwamnatocin fararen hula da kungiyoyi masu dauke da makamai.
Tushen matsalar
Masana tarihi na kallon asalin kasar Kongo a matsayin raunin da take dawwame a ciki. Abinda muka sani shi ne an fara kafa DRC a matsayin yankin Sarki Leopold II na Belgium a shekarar 1885.
Bayan kwace iko da wannan yanki, sarkin ya saka wa yankin sunan 'Congo Free State', wanda ya bayar da damar aikata munanan abubuwa ga 'yan Afirka da ke rayuwa a yankin.
An kashe miliyoyin 'yan Kongo a yayin da Leopold ke sace albarkatun kasa da na gandun dajin Kongo.
Sukar wadannan ta'annati ne ya tirsasawa Leopold barin wannan yanki ga gwamnatin Belgium a 1908. Duk da wannan sauyi, amma ba a samu saukin fuskantar zalunci ba, su ma 'yan mulkin mallakar sun dinga amfani da karfi wajen zaluntar jama'ar Kongo kamar yadda Leopold ya yi.
A ranar 10 ga watan Yunin 1960, amma sai mamayar Yammacin duniya a kasar ta ci gaba bayan Lumumba, babban dan kishin kasa marar tsoro, da ya zama firaministan kasar na farko ta hanyar lashe zabe.
Makonni bayan karbar mulki, Lumumba ya fuskanci kalubalen 'yan a ware da Yammacin duniya ke mara wa baya a kudu maso-gabashin yankin Katanga.
Ya roki Majalisar Dinkin Duniya ta ba shi gudunmowar soji, wanda suka ki amsa kiran sa, wanda ya sanya shi koma wa kamar Tarayyar Soviet.
Shugaban Kasar Kongo na wannan lokacin, Joseph Kasavubu ya dora alhakin boren kan Lumumba, ind aya kore shi a watan Satumban 1960.
Kwanaki kadan bayan hakan sai aka kama shi. A watan Janairun 1961, an mika shi ga gwamnatin yankin Katangan, wadda ba da jima wa ba ta kashe shi.
Karfin ikon Yammacin duniya
Fred M'membe, sanannen dan jarida kuma shugaban jam'iyyar ZSP ta Zambia, ya bayyana cewa kasashen yamma na yawan amfani da dabarunsu na siyasa waje dakile cigaban Afirka.
M'membe ya fada wa TRT Afirka cewa "Shugabanninmu da suka yi kokarin bin sabuwar hanya, wadda ta saba wa ta 'yan mulkin mallaka, mun ga me ya same su a tarihi. An kashe Patrice Lumumba saboda kawai ya ce arzikin Kongo na jama'ar kasar ne, sai aka raba shi da rayuwarsa."
"Yammacin duniya ya yanke hukunci kan tsarin shugabanci ma irin nasu za mu kwaikwaya. Idan muka dauki wata hanyar ta daban, sai su juya mana baya."
A 2001, binciken majalisar dokokin Belgium ya gano cewar Brussels 'Na da hannu" a mutuwar zababben firaministan Kongo na farko. Sauran bincike ya bayyana har da hannun Amurka a cikin aikata kisan gillar.
A 1965, shugaban sojo mai goyon bayan Yammacin duniya, Mobutu Sese Seko, ya hau kan mulki inda ya jagoranci gwamnatoci mafiya muni wajen zalunci da cin hanci da rashawa a duniya har tsawon shekaru 32.
A 1996 aka kifar da gwamnatin Mobutu bayan wani rikicin masu tayar da kayar baya da kasashen yankin suke mara wa baya.
Daga baya sai yki ya barke a kasar a 1997, inda aka kawo karshen sa a 2003, bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Afirka ta Kudu. Sai dai kuma, rashin tsaron ya ci gaba a gabashin DRC.
Ayyukan Lumumba
Firaministan farko na DRC a hannun 'yan a ware da Yammacin duniya ke goya wa baya ya sanya shi zama shahidin siyasa da al'adu na Afirka.
"Da wahala a ce mu fitar da tsarinmu ba tare da sanya mana takunkumi, ko a kashe mu, ko a kifar da gwamnatinmu ba." in ji M'Membe
Lumumba ya zama a sahun gaba wajen kalubalantar mamayar Yammacin duniya a Afirka. An ci gaba da gwagwarmayar neman 'yanci da kalubalantar kasashen Yamma a fadin Afirka, don samun ilhama daga wannan dan gwagwarmaya mai kishin kasa.
A fadin Afirka, tituna da dama na dauke da sunaye ko sassaken gunkin Lumumba.
A wajen jama'ar Kongo, Lumumba ya zama wata babbar alama da koyon kishin kasa, wanda ya mutu a turbar kare kasarsa. Duk da ra'ayin siyasa mabambanta da suke da shi, 'yan siyasar Kongo, na girmama akidu da ra'ayinsa.
Abinda aka gaza cimma wa a shekaru sittin da suka gabata shi ne manufifin cigaba na Lumumba ga DRC. Katsalandan din kasashen waje ne babban kalubalen d aya hana cimma wannan manufa.
Majalisar Dinkin Duniya na shirin janye dakarunta na wanzar da zaman lafiya da ke DRC bayan shekara 32.
M’membe ya yi kira ba ga DRC kawai ba, har da ga dukkan sauran kasashen Afirka da su zama masu tafiyar da al'amuransu da kansu.
"Domin kasa ta ci gaba, dole ne ya zama ta mallaki duk wasu tubala da ayyukan cigabanta, ta zama mai mallakin duk wani tsari da ke kaiwa ga cigaba." in ji shi yayin da yake tattauna da TRT Afirka.