Daga Sylvia Chebet
A farkon makon nan ne matasu suka yi fito-na-fito da 'yan sanda a babban birnin Kenya, Nairobi, a wata zanga-zanga da aka wa laƙabi da "Mamaye Majalisa", wadda ta tilasta wa gwamnati janye gagarumin shirin samar da kuɗi don kasafin da ta yi na Shilling tiriliyan huɗu (kusan dala biliyan $30) ta hanyar ƙara haraji.
Matasa masu zanga-zangar suna ganin cewa al'ummar Kenya tuntuni da ma ana cajin su haraji sama da kima, kuma suna fusace da ƙarin harajin da ake ƙoƙarin saka wa a sabon kasafin kuɗin ƙasar.
"Ba za mu yarda da ƙudurin Dokar Kuɗi ta 2024 ba. Me ya sa ake tilasta mana ala dole? Ba ma so, kuma iyakar matsayarmu kenan," cewar Wanjira Anjira, wani cikin masu zanga-zangar.
Cincirundon masu zanga-zanga suna ɗaga allon sanarwa da aka rubuta ɓaro-ɓaro: "Ka da a ƙaƙaba mana haraji", inda suke nuni da Shugaba Ruto shi ne Zakayo, wanda a harshen Swahili suna ne na mai karɓar haraji a Littafin Bible mai suna Zacchaeus.
A zahiri, zanga-zangar tana tasowa ne ba shiri, amma kuma ta hanyar kafafen sada zumunta ake haɗa ta. Da zarar matasan sun fito tituna, ba za su kauce ba duk da kame su da ake yi, da turnuƙun hayaƙin barkonon tsohuwa.
Wani rahoton 'yan sanda ya ce wani jami'insu ya jikkata, yayin da gwangwanin hayaƙi mai sa hawaye ya fashe a hannunsa.
Harajin biredi
"Mutane da dama suna kallon harajin a matsayin azabtarwa," kamar yadda masanin gudanarwa da mulki, Mohamed Guleid ya faɗa wa TRT Afrika, inda ya ce babban misali shi ne saka harajin VAT na kashi 16% kan biredi.
Guleid ya yi nuni da cewa, "Kuma ka san matsayin biredi, ba wai a Kenya ba, a duk faɗin duniya. Ka sani biredi ya taɓa kawo ƙarshen gwamnatoci a tarihi. Idan za ka tuna, juyin juya-halin Faransa da ya kawo ƙarshen mulkin Sarki Louis XVI dalilin biredi ne".
Ranar Talata, masu zanga-zangar da ke sanye da baƙaken tufafi sun yi arangama da 'yan sanda, inda suka yi ta wasan ɓuya a gine-ginen majalisar dokokin ƙasa da ke babban birnin ƙasar.
A halin yanzu, 'yan majalisa sun ba da rahoton samun tarin saƙonni a wayoyinsu, inda ake roƙon su, da kuma yi musu barazana don su kare muradun masu zanga-zanga.
"Ban san inda jama'ar Kenya suka samo lambobin wayarmu ba, kusan kowane ɗan majalisa ya samu saƙon cewa, ya yi watsi da duk dokar da aka gabatar a majalisa." cewar ɗan majalisar gundumar Mandera East, Hussein Weytan
Gwamnatin Kenya tana tsaka mai wuya. Kafin ta iya zartar da kasafin kuɗinta mafi girma, tana fuskantar zaɓi biyu: karɓo bashi ko saka haraji.
Gwamnatin ta zaɓi ƙara haraji.
Matakai wajibai
Gwamnatin ta kare batun ƙarin da ake hasashen zai kawo mata ƙarin kuɗi Shilling biliyan 346.7 (dala biliyan $2.7), wanda mataki ne da ya wajaba don rage dogaro kan ciyo bashi daga waje.
Sai dai kuma, "wasu lokutan idan gwamnati ta taɓo batun abubuwan buƙata na mutane, hakan yakan zamo matsi," a cewar Guleid, wanda kuma tsohon mataimakin gwamna ne.
A ƙarshe, gwamnati ce ta fara ja baya, inda ta dakatar da jerin harajin tun kafin majalisa ta zauna kan batun Dokar Kuɗi ta 2024.
Mambobin Majalisa za su zauna don muhawara kan ƙudurin dokar ranar Talata, amma sun dakatar da tattaunawar zuwa Laraba, dab da lokacin da fadar shugaban ƙasa ta sanar da gyararraki kan dokar haraji bayan shawarwarin da kwamitin majalisa ya bayar.
"Saboda wakilan al'umma sun saurari mutane... sun sauya ƙudurorin," Shugaba William Ruto ya faɗa a wani taro da 'yan majalisa daga jam'iyya mai mulki ta gamayyar Kenya Kwanza.
Da ba don wannan ba, za a bayar da dama ga mutane su shiga tattaunawa tsakanin muhawara a majalisa, kafin ƙudurin ya zama doka. A cewar Guleid, "jama' sun riga sun nuna matsayarsu."
Ƙuri'a a majalisa
Gwamnati na da har 1 ga watan Yuli na samar da doka wadda za ta zartar da sabon kasafin kuɗi. Majalisa za ta kaɗa ƙuri'a kan ko za ta amince da Dokar Kuɗin, wadda za ta fayyace yadda za a kashe kuɗaɗen gwamnati a shekara guda mai zuwa daga ƙarshen watan Yuni.
"Idan hakar bai faru ba, to za a samu naƙasu a lamuran gwamnati gabaɗaya, wanda ke nufin gwamnatin ba ta da kasafin kuɗi kuma ba ta da ikon kashe kuɗi," cewar Guleid, wani masani kan harkokin tafiyar da gwamnati.
Awanni bayan an fara zanga-zangar, kwamitin kuɗi na majalisa ya fitar da sanarwa mai cewa zai yi watsi da da yawa daga ƙudurorin dokar masu kawo jayayya, ciki har da haraji kan biredi da mallakar mota.
"Dokar Kuɗin an mata gyara don cire harajin VAT na kashi 16% kan biredi, da safarar sukari, da hada-hadar kuɗi, da canjin kuɗi da harajin kashi 2.5% kan motoci," cewar shugaban kwamitin, Kimani Kuria.
"Bugu da ƙari, ba za a yi ƙari kan cajin kuɗi kan tura kuɗi ta banki, da haraji kan kaya kamar man girki."
Salon 'yan Gen Z
"Abin da ya faru a Nairobi wani gagarumin abu ne da ba a taɓa gani ba a baya," cewar Guleid, inda ya yi nunin cewa a baya, yawanci jam'iyyun adawa ne ka shirya zanga-zanga.
"An saba gani mutane kamar su Raila Odinga, babban ɗan adawa suke shiryawa. Amma a wannan lokaci mutanen da ke fito na fiton matasa ne, waɗan a yanzu ake kira da 'yan Gen Z.
Masu sharyi suna ganin cewa wannan rukunin mutane a baya kamar ba su damu da siyasa ba.
Guleid ya ƙara da cewa, "Ba a saba ganin matasa ƙanana suna tattaunawa a fagen siysa ba, amma a yanzu da alama sun samu bakin magana.
"Batu ne na rayuwarmu," Njira ya jaddada, kuam ya ƙara da cewa fushin mutane ba a kan haraji ya tsaya ba. "Batu ne na yadda ake gudanar da arziƙinmu na ƙasa."
Ajandar garanbawul
Shugaba Ruto ya hau mulki ne a shekarar 2022 bisa alƙawuran farfaɗo da tattalin arziƙi, da samar da kuɗi a aljifan talakawa, amma manufofinsa na haraji sun haifar da a faɗin ƙasar.
"A bara 2023, ya gabatar da sabbin haraji da suka haɗa da ƙarin kashi 2.5% cikin ɗari a harajin zuba jari a harkar samar da gidaje, da ƙarin kuɗin da ake zuba wa a inshorar lafiya, baya ga ninka harajin VAT kan albarkatun man fetur da kashi 16%.
Hauhawar farashi a ƙasar da ke gabashin Afirka ya ci gaba da yin sama, a matakin da ya kai kashi 5.1 cikin ɗari a watan Mayu, yayin da tashin farashin abinci da mai ya kai kashi 6.2 da kashi 7.8 cikin ɗari bi-da-bi, cewar bayanai daga babban bankin ƙasa.
An shirya sake yi zanga-zanga ranar Alhamis a Nairobi, bayan da masu zanga-zangar suka bayyana rashin jin-daɗinsu da matakan amsar buƙatunsu da gwamnati ta yi kan dokar harajin da ake gabatarwa.