Watakila shekara 30 ba za su iya zama masu yawa ba a tarihin wata kasa, amma sun isa a ce a wannan lokaci kasar ta dauki hanyar makomarta.
Game da Afirka ta Kudu, shekaru talatin da kasra ta yi tun bayan samun 'yancin kai sun zama kamar hanyar neman mafita ta fuskoki da dama, da suka hada da jarrabawa da matsalolin kasa mai taso wa daga yanayin rintsi kuma take shiga sabon tsarin zamantakewa mai tafiya da kowanne bangare, siyasa mai karsashi da karfin tattalin arziki.
Amma ta yaya wannan bukata ta sabon suna da matsayi za ta karbu a kasar da ke da al'ummu mabmbanta? Amsar na iya ta'allaka ga sake bin diddigin sahun da ake a kai.
Gina Al'umma
Kwararru a fannin cigaba sun bayyana cewa a tattare da dukkan sauyin siyasar da aka samu a wannan dimokuradiyya mai aiki bisa doron kundin tsarin mulki, wanda abu daya da ba ya sauya wa shi ne aiki tare a koyaushe don ganin an raba kasar da talauci.
"Muhimmin zuba jari a fannin ilimi shi ne kafa makarantu na musamman, wadanda su ne irin su na farko a kasar," in ji Aluwani Chokoe, kakakin kungiyar Majalisar Matasan Fasahar Sadarwa, kungiya mai zaman kanta da ke fafutukar ganin an shigar da matasa cikin harkokin tattalin arziki, a wata tattaunawa da ta yi da TRT Afirka.
"Wadannan makarantu sun zarce kawai matsayin makarantun koyo da korawa, sna baiwa masu koyo damar kwarewa a fannonin lissafi, fasahar sadarwa da yanar gizon injiniyanci, kasuwanci da sana'a."
Amma duk da matakai da ke karo da juna da aka dinga dauka, ana barin bakaken fata 'yan Afirka ta Kudu a baya a fannin ilimi, wanda hakan ke janyo rashin daidaito wajen samun ayyukan yi a fadin kasar."
"Matasa na ta gwagwarmayar samun ilimi da damarmaki don inganta rayuwarsu, kuma gwamnatoci na ta kokarin magance matsalolin kasar ta hanyoyi da dama shekaru 30 da suka gabata," in ji Aluwani.
Habakar tattalin arziki
Tattalin arzikin Afirka ya habaka sosai tun bayan kawo karshen mulkin fararen fata tsiraru d akuma cire takunkuman tattalin arziki na kasa da kasa da aka saka wa kasar.
Alkaluman Bankin Duniya sun nuna cewa kudaden da kasar ke samu a cikin gida ya daga daga dala biliyan $153 a 1994 zuwa $58 a 2011, sauyi mai muhimmanci a shekaru 10 na farko bayan samun 'yancin kai.
Duk da daidaituwar habakar tattalin arzikin, an samu tsaiko wajen saurin habakar sbaoda wasu abubuw ada bullo.
A yayin da kasar za ta gudanar da zabuka a wannan shekarar, matasa na son ganin an samu sauyi sosai don dawo da kasar kan turba.
A wani rahoto na baya-bayan na da PwC suka fitar, a watan Afriilun 2024 ya yi nuni da cewa duk da kalubale da dama da kasarmu ke fuskanta, tattalin arzikinmu ya ja hankalin zuba jari kai tsaye daga kasashen waje na kusan rand 100 a 2023, daidai da kashi 1.4 na GDP din kasar, in ji Aluwani.
"Muna son ganin kokarin da zai dakatar da tabarbarewar da ake samu wajen ayyuka a birane da kauyukan fadin kasar. Haka kuma, a kassara rashin aikin yi da aikata muggan laifuka. 'Yan Afirka ta Kudu na son zama al'umma mai shan romon dimokuradiyya da samun cigaban kasa."
Raunukan da suka shude
Duk da habakar tattalin arziki da karuwar GDP sosai, har yanzu bakaken fata 'yan Afirka ta kudu na cigab ada fuskantar matsalar amfana na da tattalin arzikin kasar.
Aluwani ta ce "Har yanzu Afirka ta Kudu na cikin kasashen da ke fama da rashin adalcin samun kidade a tsakanin 'yan kasa, dalilai da dama ne suke tabbatar da hakan. Duk da kuma manufofi da aiki tukuru da ake yi. Har yanzu bakaken fata ba su da wata babbar rawar takawa a fagen juya tattalin arzikin kasar."
A ra'ayinta, a koyaushe za a dinga samun sabani da rikici tsakanin mutane mabmbantan launi matukar akwai tunanin cewar wasu sun fi wasu. "Akwai makiyan dimokuradiyya da da suka ki amincewa da dimokuradiyyar Afirka ta Kudu a matsayin fagen da kowa zai baje hajarsa ciki daidaito."
Cikin godya, wannan tunani na raguwa sosai. Matasa sun fi mayar da hankali ga samun makoma mai kyau ga Afirka ta kudu, sama da jama'a baya, wadanda har yanzu suke warke wa daga raunukan da kasar ta ji a baya."
Alwani ta yi nuni da cewar dukkan su na bukatar wanzuwa don samun cigaba.
Ta shaida wa TRT Afirka cewa "A kowace al'umma, akwai kyakkyawan rikici tsakanin nasarori da ayyukan da jama'ar jiya suka cimma da kuma burace-buracen da matasa ke da su kuma suke fatan ganin an samar a cikin al'ummunsu. Al'ummu masu nasara su ne wadanda suka yi amfani da wannan rikici ta hanya mai kyau don kawo cigaba."
A ranar 29 ga Mayu, Afirka ta Kudu za ta gudanar da zabe a karo na bakwai don zabar gwamnatin dimokuradiyya da z ata wakilci abinda al'umma ke so.
Tambayar da za a yi a nan ita ce: shin wadanda jama'a za su zaba za su iya ciyar da kasar gaba sannan ta ci gaba da yaki shaidanun jiya da na yau?