Shugabannin Afirka da ke halartar Makon Ci-gaba mai Dorewa na Abu Dhabi na 2025 (Abu Dhabi Sustainability Week ADSW) sun yi kira da a samar da tattaunawa mai tasiri da haɗin gwiwa da damar saka hannun jari, da haɗin gwiwar mutuntawa tsakanin ƙasashen Afirka da al'ummomin duniya.
An kaddamar da Makon Ci-gaba mai Dorewa na Abu Dhabi (ADSW) a cikin 2008 a matsayin "dandali na duniya ga duk wanda ke da ruwa da tsaki a makomar duniyarmu," in ji shafin intanet na taron.
Hakanan yana da nufin "nuna yadda haɗin fasahar zamani, gami da ƙirƙirarriyar basira (AI), makamashi, da ƙwarewar ɗan'adam, na iya haɓaka ci gaba mai dorewa da buɗe yuwuwar canjin tattalin arzikin dalar Amurka tiriliyan 10."
Taron na bana, wanda zai gudana daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu karkashin jagorancin shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, na da nufin "samar da ci gaba mai dorewa da ci gaban tattalin arziki".
'Muhawarar da ba za ta ƙare ba'
Taron ya hada shugabanni da yawa daga ko ina a duniya, ciki har da na Afirka da dama. Shugabannin Afirka sun sake jaddada bukatar kasashen duniya su sake jajircewa kan ajandar dorewar ci-gaban duniya.
Har ila yau, sun jaddada bukatar a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da hadewar jama'a, da kiyaye muhalli, musamman ga kasashe masu tasowa wadanda sauyin yanayi ke yi wa illa - rikicin da ke kara ta'azzara sakamakon ayyukan kasashen da suka ci gaba.
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya bayyana takaicinsa kan gibin da ke tsakanin alkawurran siyasa na tarukan da suka gabata da kuma aiwatar da ayyuka a cikin wata sanarwa a shafin X.
Kagame ya ce, "Har yanzu ba a cika alkwarin ajandar dorewar ci-gaban duniya ba, musamman ga Afirka."
“Ba a cika alkawuran siyasa da aiki ba, lamarin da ke barin mu da ci gaba da yin muhawara mara iyaka da nuna wa juna yatsa. Don cim ma burin biyun, dole ne mu yi amfani da fasaha mai araha, mai daidaitawa, da kuma tattalin arziki,'' in ji shi.
Damarmakin tattalin arziki
Ministan Masana'antu da Fasaha na Hadaddiyar Daular Larabawa, Dokta Sultan Al Jaber, yana nuna rawar da Taron ADSW ke takawa wajen sauƙaƙe haɗin gwiwar kasuwanci.
"Makon Dorewa Ci-faba na Abu Dhabi 2025 zai yi aiki a matsayin haɗin gwiwa ga shugabannin kasuwanci na duniya da masu tsara manufofi, da 'yan kasuwa da yin amfani da hanyoyin haɗin gwiwar da ke gina kyakkyawar makoma ga kowa," in ji Al Jaber a cikin jawabinsa na budewa.
Shugaban kasar Kenya William Ruto ma ya yaba da damar da dandalin ya bayar, inda ya ba da misali da wata sabuwar yarjejeniya ta tattalin arziki tsakanin kasarsa da Hadaddiyar Daular Larabawa da suka rattabawa hannu a gefen taron.
"Muna nazarin yarjejeniyar haɗin gwiwa da Hadaddiyar Daular Larabawa don tsawaita layin dogo na Standard Gauge don haɗa Kenya, Uganda da Sudan ta Kudu," in ji Ruto.
Ya kara da cewa, "A matsayin wani bangare na shirin, mun amince da gudanar da binciken yiwuwar kara wa'adin SGR saboda karfin da yake da shi na bunkasa hadin gwiwar yanki da inganta kasuwanci," in ji shi.
'Lokacin Afirka'
Shugaban kasar ya kara da cewa, ''ana sa ran Kenya za ta ninka yawan fitar da nama da 'ya'yan itatuwa da kayan marmari, da furanni, da shayi, da kofi zuwa kasashen waje fiye da sau uku.
Sai dai kuma batun da ake ta tafkawa na rashin cika alkawuran da aka dauka da rashin samun daidaiton wakilci a teburin shawarwarin duniya ya kasance babban abin damuwa ga shugabannin Afirka.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jaddada muhimmancin dogaro da kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka.
''Afirka tana da abin da ake bukata don bunkasa kanta. Muna da albarkatu da mutane da iya aiki.
"Dole ne mu sa ido a ciki don inganta kasuwanci da haɗin gwiwa tsakanin Afirka don amfanar jama'ar Afirka da nahiyar. Yanzu lokaci ne na Afirka, ”in ji Tinubu a cikin wata sanarwa.