Shugaba Tinubu ya kai ziyarar kwana uku Faransa a makon karshe na watan Nuwamba inda aka karɓe shi hannu bibbiyu. Hoto/Nigerian Government

Daga

Abdulwasiu Hassan

Faransa, wadda ta yi mulkin mallaka a ɓangare da yawa a Afirka, tana ganewa cewa nahiyar ba za ta yarda ta zama ‘yar amshin shatarta ba.

Alaƙar diflomasiyya da ƙasar ta Turai da kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara ta yi ƙasa matuƙa, inda ƙasashe kamar Senegal da Chadi suka rufe sansanin sojin Faransa a ƙasashensu.

Sun kuma yanke dangantaka ta soji da ita bayan Nijar da Mali da Burkina Faso suka yanke hulɗa da ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka.

"Chadi tamu ce, Faransa ki fita!" wannan shi ne abin da dubban masu zanga-zanga ke cewa a lokacin da suka yi zanga-zanga ranr 6 ga watan Disamba a babban birnin Chadi N'Djamena da kuma birnin Abeche.

A makon da ya gabata, gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa zata kawo karshen yarjejeniyar tsaro da Faransa domin tabbatar da “cikakken ‘yancin kanta” tare da sake bayyana alaƙarta kan buƙatunta.

Yayin da ƙin jinin Faransa ke ƙara yaɗuwa a yankin Sahel, Faransa tana ƙoƙarin matsa kusa da ƙasar da ta fi yawan mutane a nahiyar Afirka, Nijeriya, lamarin da mutane da yawa a yankin suke ganin ƙarfafa alaƙa da ƙasar da ta taɓa mulkin mallaka yana cike da hatsari.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu shi ne shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin Yammacin Afirka( ECOWAS) kuma manazarta na ganin yunƙurin Faransa na ƙarfafa alaƙa da Nijeriya ƙoƙari ne ƙasar da ta taɓa mulkin mallaka ta tabbatar da ƙarfin fada ajinta a yankin.

Jim kadan bayan ziyarar Tinubu zuwa Faransa sai aka sanar da cim ma yarjejeniyar ma'adinai tsakanin kasashen biyu:Hoto/Nigerian Government

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kai ziyarar kwana uku Faransa a makon karshe na watan Nuwamba inda aka karɓe shi hannu bibbiyu.

Takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, ne ya jagoranci tarbar da aka yi masa tare da wallafa bayanan diflomasiyya kan kafafen sada zumunta wanda wasu ke ganin ya wuce gona da iri.

Macron ya kasance ɗalibi mai neman kwarewa a ofishin jakadancin Faransa da ke Legas a shekarar 2002 a lokacin da Bola Tinubu ke gwamna a jihar ta Legas.

Sai dai kuma, tarbar da aka yi wa Tinubu da kuma yarjejeniyoyin da aka cimma sun nuna cewa haduwarsu ya fi ƙarfin sabunta abokantakar da aka ƙulla a Legas kawai.

Ana nuna tsabar ɓacin rai game da ƙara danƙon zumuncin da Nijeriya ke da Faransa, wadda mutane da dama ke yi wa kallon ƙasa mai tsaokanar zalunci.

Dokta Aminu Hayatu, wani mai binciken kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano, yana ganin ƙasar mafi ƙarfi a Yammacin Afirka tana tsaka mia wuya.

"Faransa tana fuskantar wani yanayi mawuyaci a Afirka yayin da take sake ƙoƙarin sake mallakar, abin da a zamanin yanzu ke nufin sake dabara domin cin ribar yadda tsarin duniya ke sanuyawa.

"Ba Faransa ba ne kawai; wasu manyan ƙasashen Yammacin duniya ma suna hakan," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Yayin da Nijeriya ka iya samun fasahar Farasan, akwai yiwuwar Faransa ta yi amfani da damar domin dabarar samun abin da take so," in ji shi.

Tsoro

Yarjejeniyar da aka cim ma a lokacin da ziyarar ta Shugaba Tinubu ta nuna cewa ƙasashen biyu "za su haɗa kai wajen bincike da horarwa da kuma musayar ɗalibai da kuma musayar kwarewa ".

Tsarin kuma ya haɗa da fitar da albarkatun ƙasa ta Nijeriya.

‘Yan Nijeriya da suka san tarihin azabtarwar mulkin mallaka na baya da kuma tasirin Farasa bayan mulkin mallaka a wasu sassan Afirka suna kaffa-kaffa da duka wata yarjejeniyar da aka ƙulla da ko wace babbar ƙasa daga Turai.

Jim kaɗan bayan an bayyana yarjejeniyar, ‘yan Nijeriya da yawa sun nuna rashin amincewarsu da kuma tsoro kan yiwuwar Faransa ta karɓe iko da fannin albarkatun ƙasa na Nijeriya.

Lamarin ya tilasta wa gwamnatin Nijeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi ƙoƙarin rage tsoron hatsarin.

"Yan Faransa ba za su karɓe iko da fannin ma’adinan Nijeriya ba," a cewar babban mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai, Sunday Dare, a wata sanarwa.

Sai dai kuma, akwai tsoron a Nijeriya, musamman a arewacin ƙasar wadda ke da iyaka da Nijar, ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke jin zafin mulkin mallakar Faransa da kuma abin da ya biyo bayansa.

Darasi daga Sahel

Ra’ayin da ya fi rinjaye cikin ‘yan kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar shi ne ci-gaba da kasancewar Faransa a ƙasashen ya ƙara yawan matsalolin tsaronsu ne maimakon rage su.

Tarihin Nijeriya da Farasansa dai ya sha bamban, amma tunani game ababen da suka faru a yankin cikin gomman shekarun da suka wuce na da tasiri kan ra’ayin jama’a a yankin.

Alaƙar diflomasiyya da ƙasar ta Turai da kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara ta yi ƙasa matuƙa.

Nijeriya dai Birtaniya ce ta yi mata mulkin mallaka, maimakon Faransa wadda ta yi wa ƙasashen da ke yanke hulɗa da ita mulkin mallaka.

"Ko wace alaƙa na da tarihi da kuma siga. Dangantakar waɗannan ƙasashen (Mali da Burkina Faso da kuma Nijar) da Faransa ta sha bamban da dangantakar Nijeriya," kamar yadda Abdulaziz Abdulaziz, babban mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan watsa labarai ya shaida wa TRT Afrika.

"Kasancewar waɗannan makwabtan suna da matsala da Faransa ba ta kai hujjar da za ta mu samu matsala da ita ba. Ba haka lamarin ya ke ba," a cewarsa.

Wasu manazarta sun ce Nijeriya ka da ta ɗauki alaƙarta da Faransa haka kawai, saboda dangantakar za ta yi tasiri a wajen ƙasar.

"Idan sauran ƙasashe a yankin suka ga kusantar Nijeriya da Faransa a matsayin wata barazana a gare su, zai iya ƙara tayar da hankali da gasa a yankin," in ji Dakta Hayatu.

Manazarta na ganin duk da cewa Faransa na da buri a kan Nijeriya, ƙarin ƙin jinin Faransa da kuma tafiyar son Afirka a yankin na nufin tsohuwar mai mullkin mallakar za ta ci gaba da shan wahala a yankin.

TRT Afrika