Matsayar Amurka ya harzuka ƙasashen Afirka da cibiyoyinsu. Hoto: AP  

Daga Susan Mwongeli

Ɗaɗaɗɗen yunƙurin AfirKa na neman kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya samu goyon baya da ba a yi tsammani ba daga Amurka gabanin babban taron majalisar karo na 79 da aka gudanar a birnin New York a cikin watan Satumba.

Sai dai farin cikin mamakin bai ɗauki lokaci ba tun da dai sanarwar ta zo da wani sharaɗi ne.

Yayin da Amurka ta ƙuduri aniyar mara baya ga matakin na kasashen Afirka na samun akalla kujeru biyu na din-din-din a kwamitin sulhun, ta dage waɗanda suke tunanin shuga kada su yi tunanin za su sami gurbi a kujerar na ƙi ta MDD.

"Ba za mu so mu bar ikonmu na hawa kujerar na ƙi ba... Fadada ikon kujerar na ƙi a fadin hukumar zai sa majalisar ta kara zama mara tasiri," in ji Linda Thomas-Greenfield, jakadiyar Amurka a MDD.

Matsayin na Amurka ya harzuka kasashen Afirka da cibiyoyinsu, inda da yawa ke bayyana hakan a matsayin cin fuska ga nahiyar.

Arikana Chihombori-Quao, tsohuwar jakadiyar Tarayyar Afirka a Amurka, ta yi imanin cewa bai kamata Afirka ta “ɓata lokaci” na samun kujeru na dindindin a Kwamitin Sulhu ba ba tare da ba ta ikon hawa kujerar na ƙi ba.

"Mun gaji da wannan abu," in ji ta, tana mai bayyana takaicin nahiyar da ke son fiye da ɓaɓatun da ake yi don samun biyan bukatarta.

To wai, me ya sa samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu ke da muhimmanci?

A taƙaice dai, shi ne sashe mafi tasiri a Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya ƙunshi zaɓaɓɓun ƙungiyar ƙasashe masu ikon yanke shawarar abin da sauran ba za su iya ba.

Majalisar Dinkin Duniya na da mambobi 193, amma kasashe biyar ne kawai ke zama mambobin dindindin a Kwamitin Sulhun da ke da karfin iko na kaɗa ƙuri'a kujerar na ƙi. Tare da Amurka, mambobin wannan keɓantaccen sashe su ne Birtaniya da Rasha da China da Faransa.

Kowannensu na da hakkin yin watsi da duk wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da bai amince da shi ba, kuma shi kenan an manta da wannan kuduri.

Fadada ikon kujerar na ƙi a fadin hukumar zai sa majalisar ta kara zama mara tasiri," in ji Linda Thomas-Greenfield, jakadiyar Amurka a MDD. 

Chihombori-Quao tana matuƙar mamakin cewa kasashe biyar ne za su iya yanke wani hukunci kan ƙasa fiye da 188 idan aka ƙidaya.

"Ina ganin abin kunya ne a ce MDD za ta iya tattaunawa da gaske, ta sa kasashe su yi muhawara kan ko ya kamata mu fadada kwamitin sulhu ko a'a, sannan a ci mutuncinmu ta hanyar cewa, 'Oh! zo ku zauna a teburin amma ku zama kurame kamar yadda kuka kasance shekaru aru-aru. Hakan ba abin yarda ba ne," in ji ta.

Kasashe 54 da ke da al'umma sama da biliyan 1.5, Afirka ita ce babbar kungiyar masu kada kuri'a a babban taron. Shugabannin kasashen Afirka dai na ta kokarin ganin nahiyar ta samu kujeru na din-din-din a kwamitin sulhu tare da ƙin amincewa da ƙudurin da babban taron majalisar ya dauka ba ya rataya a wuyan kasashen.

Kamar yadda shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana, wannan shi ne ma’aunin rashin adalci a tsarin duniya.

Ya ce, "Samar da makomar tsaron duniya a hannun wasu zaɓaɓɓu yayin da akasarin al'ummomin duniya ne ke ɗaukar nauyin barazana iri-iri, rashin adalci ne, rashin adalci, da rashin dorewa," in ji shi.

Shugaban kasar Kenya William Ruto yana kallon abin a matsayin rashin gaskiya cewa wata cibiya ta duniya a karni na 21 za ta iya ware kasashen Afirka 54 tare da barin kasashe biyar su ƙi amincewa da shawarar da suka rage.

Lokacin da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya, yawancin kasashen Afirka sun kasance karkashin mulkin mallaka na danniya. Abin da ke daure kai ga mafi yawan masu lura da al'amura shi ne yadda kungiyar ke ci gaba da jajircewa wajen tunani da aiki dangane da nahiyar.

Shugaba Julius Maada Bio na Saliyo ya ce "Kusan shekaru 80 da kafa kwamitin sulhun ya makale a cikin rudani, rashin daidaiton tsarinsa na rashin adalci ne kuma ya yi hannun riga da hakikanin abubuwan da ke faruwa a yanzu, wanda ke kawo cikas ga haƙƙinsa da ingancinsa," in ji Shugaba Julius Maada Bio na Saliyo.

A halin yanzu dai batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka ke da kashi 60-70% na ajandar kwamitin sulhun. Amma duk da haka, kwamitin yanke shawara ba ya bai wa nahiyar damar yin magana a kan wadannan batutuwa, da daukar matsayi na son kai.

Rashin tsari

An kafa Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1945, bayan Yakin Duniya na Biyu, tare da babban nauyi na rigakafi da magance rikice-rikice. Manufar ita ce a guje wa kura-kuran waɗanda suka gabata, wato na Ƙungiyar Ƙasashen Duniya.

Kwamitin Sulhu ya kasance bangaren da ya fi tasiri a Majalisar Dinkin Duniya. Tana da mambobi 15, 10 daga cikinsu ba su zama na dindindin ba tare da ikon hawa kujerar na ƙi ba. Mambobin dindindin sun kasance iri ɗaya tun lokacin da aka kafa majalisar.

Ana zabar mambobin da ba na dindindin ba ne na tsawon shekaru biyu ta babban taron a bisa tsarin karba-karba tsakanin kasashe daga kungiyoyin shiyya-shiyya a MDD.

Afirka na da kujeru guda uku wadanda ba na dindindin ba, a halin yanzu da suka haɗa da Algeria da Saliyo da Mozambique.

Wasu manazarta sun ce fadada majalisar na iya kawo daidaito da kuma sanya ta zama mai wakilci a duniya ta yanzu. 

A wasu lokuta, Kwamitin Tsaro na iya ba da izinin yin amfani da karfin soji a kan wani mai cin zarafi. Amma ga yadda abin yake: idan ɗaya daga cikin ƙasashen da ake kira P5 ba ta son lamarin, to kawai sai ta hau kujerar na ƙi.

Amitabh Behar, babban daraktan Oxfam na kasa da kasa ya ce "Yana da matukar muhimmanci cewa ikon rike da alkalami a cikin kwamitin sulhu ya zama dimokiradiyya. Ba za ku iya ci gaba da samun wata ƙasa ta P5 mai rike da madannin nukiliya ba kuma ke da ikon tsarawa da kuma kudurori."

A bisa ƙa'ida, kungiyar Tarayyar Afirka ta goyi bayan kawar da karfin hawa kujerar na ƙi. Idan P5 ta ci gaba da rike madafun iko, kujeru biyu na dindindin tare da dukkan iko ya kamata su zo Afirka.

Rarrabuwar kawuna

Duk da cewa shi ne mafi karfi a Majalisar Dinkin Duniya, kwamitin sulhun kuma ya fi samun rarrabuwar kawuna.

Mambobinsa, musamman Rasha, China da Amurka, akai-akai ba sa jituwa da juna kan manyan kudurori da ka iya tasiri a duniya.

Wasu manazarta sun ce fadada majalisar na iya kawo daidaito da kuma sanya ta zama mai wakilci a duniya ta yanzu.

Yarjejeniyar Ezulwini, wacce aka sanya wa sunan wani kwari a Tsakiyar Eswatini (wacce ita ce Swaziland), ta isa ne a shekara ta 2005 don neman wakilcin Afirka a kwamitin sulhu ta hanyar zama mamba na dindindin.

Ba kasashen Afirka ne kadai ke kokarin fadada kwamitin sulhun ba. Wannan kamfen ne na ci gaba a duniya wanda kasashe irin su Turkiyya ke jagoranta.

Hakan Fidan, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ce "ana bukatar cikakken garambawul a Majalisar Dinkin Duniya, musamman ma a kwamitin sulhu. Duniya ta fi biyar girma. Muna bukatar mu mayar da tsarin yanke shawara a MDD."

"Kudurorin da aka amince da su da gagarumin rinjaye a zauren Majalisar ba za su iya aiwatar da su ba saboda kwamitin sulhun. Ba za a iya barin zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa bisa ga ra'ayin wani sashe da ya ƙunshi kasashe masu iyaka."

Rikitaccen tsari

Dole ne a sake fasalin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya don fadada kwamitin sulhu. Wasu sun ce aiki ne mai wahala, ko da yake ba za a ce zai yiwu ba.

Dole ne kashi biyu bisa uku na Babban taron su amince, kuma duk mambobin da ke rike da ikon hawa kujerar na ƙi to dole ne su kasance sun amince.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana kyakkyawan fata. "Ina ganin duk wadannan abubuwa za su iya yiwuwa, kuma ina fatan samun ci gaba a dukkansu. Ina da shakku kan yiwuwar soke zaben na ƙin amincewa. Wannan ba yana nufin ina son hakan ba," in ji shi.

TRT Afrika