Daga Nuri Aden
Sashin shari'a na Jami'ar Boğazici da ke birnin Istanbul ya gudanar da wani taron kwanaki biyu a ƙarshen makon da ya wuce, wanda ya hada manyan masana harkokin shari'a sama da 100 don sake yin nazari kan tsarin shari'a na kasa da kasa game da kisan kare dangi da Isra'ila ke cigaba da yi Gaza.
Na'eem Jeenah, marubuci kuma babban mai bincike a Cibiyar nazarin dabaru na Mapungubwe da ke Afirka ta Kudu, ya gabatar da wata kasida da ta yi duba kan karin abubuwan da ke faruwa a Falasdinu a matsayin abin da ya ƙira '' Tsarin Afirka na kawar da mulkin mallaka.''
Cibiyar Afirka ta kare hakkin bil adama da al'umma ta fitar da wata sanarwa ta musamman game da batun Falasdinu da kuma yadda Ƙungiyar Tarayyar Afirka take adawa yaduwa tare da neman hanyoyin kifar da kuma kawar da tasirin yahudawa daga Afirka,'' kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka a wani bangare na taron da aka gudanar a ranar 3 zuwa 4 ga watan Agusta.
An wa taron take da '' sake nazari kan dokokin kasa da kasa bayan Gaza''
Kasidar Jeenah dai ta yi nuni da karar da Afrika ta Kudu ta shigar a Kotun Duniya ta ICJ a ranar 29 ga watan Disambar bara kan kisan kiyashin da Isra'ila ke ci gaba da yi wa Falasdinawa a Gaza.
Kawo yanzu dai Isra'ila ta kashe Falasdinawa kusan 40,000 a Gaza tun daga soma hare-harenta a watan Oktobar bara.
Darussa na gaba
Alkalin babbar kotun Western Cape Siraj Desai mai ritaya, sannan wanda ya shugabanci Afirka ta Kudu wajen shigar da karar, ya bayyana bukatar daukar matakin doka kan take hakkin ɗan adam a Gaza tare da tsara manufofin shari'a da na siyasa a nan gaba.
''Wannan taro kan shari'a, masana sun hadu domin ba da gudummawarsu wajen gina sabon tsarin doka da kuma kafa manufofin siyasa da shari'a na shekaru masu zuwa ba wai ga Falasdinu kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya a nan gaba,'' in ji shi.
Ƙasashe da dama kamar Turkiyya sun goyi bayan karar kisan kiyashin da Afrika ta Kudu ta shigar kan Isra'ila a kotun ICJ.
"Wannan ya kara nauyin shari'ar da ke gaban kotun ICJ na cewa, a yanzu Falasdinu ta zama kasar da ake yi wa mulkin mallaka," in ji shi
Richard Falk, tsohon wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin ɗan Adam a Falasdinu da aka yi wa ƙawanya, ya bayyana ra'ayinsa a wani madu'i kan ''Kalubalan Gaza: Shin dokokin duniya na da muhimmanci idan har ba za a iya aiwatar da su ba?"
Zai sani, kasancewar Isra'ila ta kore shi a lokacin aiwatar da rahoton take haƙƙin ɗan'adam a Gaza.
Micheal Lynk, wani tsohon wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin ɗan Adam a Falasdinu da aka mamaye, ya tabo batun haramtacciyar matsugunan Isra'ila a Yammacin Gabar Kogin Jordan da kuma wariyar launin fata da suka saba yarjejeniyar Romaniya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya.
Manyan maudu'ai kamar "Adalci ga Falasdinu da tasirin adalcin Kotun Duniya", da "Dokar jinƙai ta Duniya: Samun dama da Hakkoki da guraben zamani da na rayuwar Gaba",da kuma "Hakkokin zamantakewa da tattalin arziki a cikin yankunan Falasdinu da aka mamaye" su suka fi ɗaukar hankali a taron na sake nazarin dokokin kasa da kasa, don tabbatar da cewa ya yi aiki daidai da sauran ƙasashen duniya, tare da mai da hankali kan laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.
"Akasarin 'yan Afirka ta Kudu sun yi Allah wadai da kisan kiyashin saboda mutanen Afirka ta Kudu saboda wannan kisan kiyashin hari ne kai tsaye ga Falasɗinawa," in ji Desai.
Everisot Banyera, wanda farfesa ne a Jami'ar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a sake sauya fasalin tsarin dokoki na ƙasa da ƙasa ta hanyar haɗa duka masu ruwa da tsaki a wurin ɗaya "domin su yi aiki a kanmu".
A cewarsa, abin da za a fara shi ne watsi da tunanin cewa wannan wani abu ne da ake fata.
"Bai kamata mu samu yanayi ba wanda mutane ƙalilan ne za su yi amfani da iliminsu da ƙwarewarsu da iliminsu na shari’a su samar da dokokin ƙasa da ƙasa waɗanda za su yi aiki a kanmu baki ɗaya.
"Idan dokokin za su yi aiki a kanmu baki ɗaya, ya zama dole mu zauna a kan teburi a ji ra’ayinmu," in ji Banyera.
'Afirka ba za ta taɓa samun 'yanci ba har sai Falasɗinu ta samu'
Ya yi nuni da yadda Falasɗinu ke ƙara samun goyon baya a faɗin duniya a matsayin wani muhimmin abu.
Jenah, wanda ya gabatar da takarda kan "Sake Tsara Dokokin Kasa da Kasa: Ra'ayin Kudancin Duniya da Kalubale", ya ce ya kamata a kula da matsalolin Falasdinu a matsayin wani bangare mafi girma na kawo karshen mulkin mallaka.
"Afirka na da rawar da za ta taka wurin wurin kawo ƙarshen wannan lamarin," a cewarsa. "Kawar da mulkin mallaka a Afirka ba zai ƙare ba har sai Falasɗinu ta samu 'yanci, haka kuma neman 'yancin Falasɗinu neman 'yanci ne ga Afirka."
Babban mai binciken yana mayar da hankali kan tarihin dangantaka mai ƙarfi tsakanin "Masu gwagwarmayar ƙwato 'yancin Afirka da na Falasɗinu a matsayin abin koyi na ci gaba da tausaya wa al'ummar Gaza masu fama da wahala.
Jeenah ya bayyana damuwa kan rashin dakatar da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza kan cewa zai kara sanya kwarin gwiwa ga sauran kasashe masu tada kayar baya a duniya, kuma kasashen Afirka na iya fuskantar illa.
"Muna son ganin duniyar da ke tattare da adalci na 'yancin ɗan adam da kuma kyautata haƙƙin zamantakewa da tattalin arziƙin ga mutanen da aka sani".
"Sauran wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron sun hada da Balakrishnan Rajagopal, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin samun isassun gidaje, da Hilal Elver, tsohon mai ba da rahoto na Majalisar Dinkin Duniya kan hakkin abinci.
Sun ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza tare da nuna alhininsu kan irin wahalar da Falasɗinu take sha.