Daga Charles Mgbolu
Bayan yada bidiyon masu hakar ma'adanai da suka mutu a Afirka ta Kudu a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, mahukunta na rige-rigen tabbatar da kubutar da waus mahakan a wajen hakar ma'adanan zinare da ke kusa da Stilfontein don kubutar da wadanda suke raye.
Aikin ceton ya biyo bayan jajircewa da gano wasu masu hakar ma'adanai a shekarar da ta gabata, wanda ya janyo saka bayar da taimako daga Ma'aikatun 'Yan sanda da Albarkatun Kasa da Makamashi.
Jami'an ma'aikatu sun ziyarci yankin a ranar Talata don shaida yadda aikin ceton ke gudana saboda girman lamarin.
Amma a gefe guda na aikin ceton ana wata muhawara: Waye zai biya kudin aikin ceto mutanen?
Tsadar aikin
Sashen Kula da Albarkatun Kasa ya yi hasashen cewa aikin ceto mutanen za lashe kudi kimanin dalar Amurka 626,332, wanda ya janyo muhawarar wa zai biya wannan kudin; gwamnati ko mamallakan mahakar, Buffelsfontein Gold.
Ana sa ran wata Kotun Kundin Tsarin Mulki ta Afirka ta Kudu za ta yanke hukunci kan batun a wata rana da a bayyana ba.
Kalubalen ba na kudi ba ne kawai, har da na rayukan jama'a da za a iya rasa wa.
Rahotannin kafafen yada labarai na yankin sun ce sama da gawarwaki 10 aka ciro a ranar Litinin, inda bidiyon da Kungiyar Ma'aikatan Masana'antu ta Afirka ta Kudu (GIWUSA) ta fitar yake da munin kallo inda aka ga an nade gawarwakin a wasu buhuna.
"Tsawon kwanaki hudu, muna ta samun bidiyo daga karkashin kasa inda masu hakar ma'adanan suke, wanda ke bayyana mummunan yanayi," Mametiwe Sebei, shugaban GIWUSA kumalauyan kare hakkokin dan adam, ya fada wa manema labarai a Stilfontein."
Fifikon gwamnati
A yayin da ake jimamin ibtila'in, Afirka ta Kudu ta bayyana cewa wani kamfanin ceton jama'a mai zaman kansa ya fara aikin kubutar da mahakan da lamarin ya rutsa da su, inda 'yan sanda suke cewar abinda gwamnati ta bai wa fifiko shi ne a kubutar da su da ransu.
Kamfanin mai zaman kansa da ba a bayyana sunansa ba ya aika da babban keji zuwa cikin mahakar da ke kusa da Stilfontein, kilomita 140 arewa maso-yamma da Johannesburg, a ranar Litinin don hanzarta aikin ceton, in ji tashar sadarwa ta kasar SABC.
"Za mu iya tabbatar muku da cewa injin na aikin. Ya dakko mutane bakwai," in ji Mzukisi Jam, na Kungiyar Fararen Hula ta Afirka ta Kudu yayin zanta wa da manema labarai a mahakar.
"Ma'aikatun na aiki tare da mamallakan mahakar ma'adanan da kuma wani kamfani da ya kware a ayyukan ceto a mahakar ma'adanai don kammala shirin aikin, ciki har da matakan kariya da lokacin da ake sa ran dauka ana aikin," in ji SAPS a wata sanarwa.
Jami'an gwamnati da suka ziyarci mahakar ma'adanan a ranar Talata sun tabbatar da wanzuwarsu don "shaida yadda aka fara aikin" da ke manufar "tabbatar da dukkan wadanda ke hakar ba bisa ka'ida ba sun kubuta.
Dadaddiyar matsala
Hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da a kasar ake kira "zama zamas" (ma'ana "'yan buga-buga" a yaren Zulu), na addabar Afirka ta Kudu tsawon shekaru.
Ana hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba saboda talauci da rashin ayyukan yi, mutane da dama na jefa rayuwarsu cikin hatsari a yayin neman zinare.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa akwai wasu kungiyoyin mata-gari da ke rike da iko da wasu wuraren hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.
Lamarin na Stilfontein ya ta'azara a shekarar da ta gabata a lokacin da daruruwan masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, da ke tsoron za a kama su a yayin farmakin 'yan sanda, sun gudu don buya a cikin mahakar.
A kokarin tirsasa musu fitowa waje, mahukunta suka hana a kai musu abinci da abin sha.
A yayin da mahukunta ke sa ran ciro dukkan mutane a raye, yanayin nayyana irin babban kalubalen da ke tallare da Afirka ta Kudu, matsalar da ke da alaka da matsin tatalin arziki da munanan ayyuka.