Daga Sylvia Chebet
Labarin sake dawo da fitar da man fetur da Sudan ta Kudu ke yi, ya sany farin ciki a zuƙatan al'ummar kasar wadda ita ce sabuwar ƙasa a duniya.
An dakatar da sufurin jirgin dakon ɗanyen mai a Sudan ta Kudan kusan shekara guda bayan da yaƙin da ake yi a makwabciyarta Sudan ya jawo fasa wani muhimmin bututun mai, lamarin da ya tursasa dakatar da Sudan ta Kudufitar da manta zuwa kasuwannin duniya.
Kasar ta Gabashin Afirka wadda ba ta da teku tana jigilar mai zuwa kasuwannin duniya ne ta tashar jiragen ruwan Sudan da ke gabar Tekun Maliya, inda Sudan din take karɓar wasu kuɗaɗe a matsayin na jigilar kayayyaki.
Babban mai ba da shawara kan tattalin arziki a Sudan ta Kudu Dr Abraham Maliet Mamer ya shaida wa TRT Afrika cewa "Mun yi matukar farin ciki da ganin madogarar tattalin arzikinmu ta dawo."
"An yi murna a titunan Juba da sauran sassan kasar lokacin da aka fara aikin," in ji shi, ya kara da cewa: "Lokaci ne da muka dade muna jira."
Ga 'yan Sudan ta Kudu, wannan ci gaban ba kawai zai haifar da karin kudaden shiga ga gwamnati ba, har ma da kudaden da ke shiga aljihunsu.
“Mutanen da ba a biya su ba kusan shekara guda, musamman ma masu yi wa gwamnati aiki, yanzu za su rika samun albashinsu kamar yadda aka saba,” in ji masanin tattalin arzikin.
Rashin biyan albashi
Ba kowa ne zai iay jure rayuwa ba tare da biyan albashi ba na shekara guda, kuma ga dukkan ma’aikatan kasar, hakan abin mamaki ne, in ji Mamer.
Ya kara da cewa, al'ummar ƙasar sun yi matuƙar haƙuri da nuna juriya yayin da ƙasar ta shiga cikin wannan mawuyacin hali.
"Ka sani, mun fito daga dogon yaƙi, dukkan mu mun samu juriya da kishin kasa."
Amma ainihin abin da ya sa mutane da yawa suka rayu tsawon kwanaki da watanni ba tare da samun kudin shiga ba ya samo asali ne daga al'adar al'ummar ƙsar ta haɗin kai wajen nuna juriya tare.
"Su ('yan Kudancin Sudan) suna kyautata wa junansu... Don haka ko da mutane ba su samu albashi ba, suna iya ci gaba da zama a cikin tsarin jama'a, kananan 'yan kasuwa sun kasance suna kula da iyalai da 'yan'uwa har ma da ma'aikata da abokai," in ji shi.
Tun a watan Fabrairun 2024, lokacin da aka lalata wani bangare na bututun mai a lokacin yakin Sudan, 'yan Sudan ta Kudu sun ci gaba da cika alkawarin da gwamnatinsu ta dauka, suna ganin cewa rufewar na wucin gadi ne.
Tattalin arziki ai tangal-tangal
Sudan ta Kudu mai yawan jama'a kusan miliyan 12, ta karbe kusan kashi uku cikin hudu na arzikin man fetur daga Sudan lokacin da ta balle ta kuma sami 'yancin kai a shekarar 2011.
Duk da arzikin man fetur da kasar ke da shi, kasar ta yi kokarin ganin ta samu gindin zama, da yaki da tashe-tashen hankula na kabilanci, da rashin kwanciyar hankali na siyasa, da fatara, da bala’o’i.
"Mun san cewa tattalin arzikinmu yana shan wahala," in ji Puot Kang Chol, ministan man fetur na Sudan ta Kudu a wani taron manema labarai a Juba a ranar 7 ga Janairu.
Ya kara da cewa, "Mun yi imanin cewa, da gobe za a dawo fitar da man fetur zuwa kasashen waje, albarkatunmu za su dawo mana."
Ministan ya bayyana cewa, za a yi ne a hankali, inda za a fara shirin kaiwa ganga 90,000 a kowace rana.
Chol ya ce "Wannan shi ne abin da bututun zai dauka a kashi na farko. Bayan haka, idan muna da karfin haɓaka fiye da haka, za mu yi hakan."
Gabanin fashewar bututun, kasar na samar da danyen mai sama da ganga 150,000 a kowace rana, a cewar kididdigar makamashin duniya.
Ana sa ran sake dawo da hako mai zai samar da ci gaban da ake bukata ga tattalin arzikin da ya durkushe.
"Ka sani, sama da kashi 90% na kudaden shigarmu suna zuwa ne daga man fetur, don haka za ku iya ganin tasirin," in ji Mamer.
Kudaden shiga da ake tsammani
Duk da tashe-tashen hankula a kasuwannin danyen man fetur na duniya, Sudan ta Kudu na shirin samar da kusan dala miliyan 400 a duk shekara daga kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje.
"Kuma dala miliyan 400 ya ishe mu mu yi dukkan laluranmu da biyan ma'aikatanmu da kudin tsaro, har ma da zaman lafiya. Zaman lafiya na bukatar kudi mai yawa," in ji masanin tattalin arzikin.
Magance yakin Sudan cikin lumana, wanda aka fara a watan Afrilun 2023, zai iya amfanar Sudan ta Kudu matuka.
Fitar da mai ba tare da samun tsaiko ba zuwa kasuwannin duniya zai samar da kudaden shiga akai-akai da inganta masana'antu kamar noma, da ƙere-ƙere da ma'adinai.
"Don haka ne muke son zaman lafiya a yankin, domin mu ci moriyar albarkatunmu... yaki ba abu ne mai kyau ba. Yana lalata ababen more rayuwa da al'adu, da rayuka." Mamer ya kara da cewa.
"Idan abubuwa suka yi kyau, za mu iya gina matatar da za a yi amfani da su a cikin gida, saboda a halin yanzu muna fitar da danyen mai sai kuma mu shigo da tattace, wanda ke da tsada."
Fitar da tattacen mai zuwa kasashe makwabta, kamar Habasha da Kenya da Uganda da Sudan, da Somaliya, zai zama babbar nasara.
Hakan zai kara habaka tattalin arziki ba a Sudan ta Kudu kadai ba har ma a yankin kusurwar Afirka.