Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta ƙara buɗe hanyoyin samun bashi ga ‘yan ƙasar da ma masana’antu domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar a cikin sabuwar shekarar 2025.
A jawabinsa ga ‘yan ƙasar wanda ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi wannan ne ta hanyar kafa wani kamfani da zai kasance asusun tabbatar da biyan bashi na ƙasa wato National Credit Gurantee Company domin rage hatsarin ba da bashi ga bankuna da kamfanoni.
“Kamfanin da ake sa ran zai fara aiki kafin tsakiyar shekara zai kasance na haɗin-gwiwa ne tsakanin ma’aikatun gwamnati kamar bankin masana’antu da hukumar ba da bashi ga mutane (Nigerian Consumer Credit Corporation) da kamfanin zuba jari na Nijeriya da ma’aikatar kuɗi ta Nijeriya da ‘yan kasuwa da kuma hukumomin ƙasa da-ƙasa,” in ji shugaban.
“Wannan matakin zai ƙarfafa aminci a tsarin kuɗin ƙasar tare da ƙara hanyar samun bashi da kuma tallafa wa waɗanda ba su cika samun dama ba irin su mata da matasa. Zai kawo ci-gaba da farfaɗo da masana’antu da kuma inganta rayuwar al'umarmu,” a cewar Tinubu.
Kazalika shugaban ya ce gwamnati za ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa hauhawar farashi ta ragu daga kashi 34.6 cikin 100 zuwa kashi 15 a cikin 100 a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka harkar noma tare da inganta haɗa muhimman magunguna a cikin gida.
Shugaban, da ya nemi ‘yan ƙasar su goya masa baya wajen tabbatar da cewa tattalin arziƙin ƙasar ya kai na dala tiriliyon ɗaya, ya ce dole ‘yan ƙasar su inganta biyayyarsu ga ƙasar domin ta iya cim ma muradunta.
“Gaskiyar ‘yan ƙasa da kuma amincewarsu da ƙasar na da muhimmanci wajen nasarar Muradun Sabon Fata,” in ji shugaban wanda ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da halayen da suka kamata ‘yan ƙasar su kasance suna da su.
Ya ƙara da cewa shi zai ƙaddamar da wani shrin wayar da kan jama’a a shekarar 2025 wanda zai mayar da hankali kan kishin ƙasa da kuma son ƙasa ta yadda waɗanda suke gwamnati da sauran ‘yan ƙasa za su yarda da juna tare da haɗa kai.