Dogayen bishiyoyin dabinon na nesa da fagen daga na kasar Sudan, amma illar yakin ta baibaye ko'ina, inda manoma suka yi tsuru-tsuru suna neman masu saye a kakar dabino ta bana.
Farashi ya karye a kasuwar dabino, bangaren tattalin arziki na baya-bayan nan da ya samu babbar illa sakamakon yakin da ake yi a kasar ta arewacin Afirka.
A kowacce bazara, har zuwa watan Satumba manoman dabino a Sudan na girbe shi daga kan bishiyoyi, inda suke samun kudaden da za su rike su tsawon watanni.
Amma shekaru biyar bayan fara yaki tsakanin bangarorin Sudan da ke rikici da juna, an lalata fasalin tattalin arzikin kasar, kuma "masu sayen dabino na tsoro", in ji wani manomi Fatih Al Badawi mai shekara 54 yayin tattaunawarsa da AFP.
Sudan ce kasa ta bakwai a duniya da ke kan gaba wajen fitar da dabino zuwa kasashen waje, inda take noma sama da tan 460 a kowacce shekara, kamar yadda hukumar abinci da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Ana jira tare da sauraron ganin me zai faru a wannan shekarar, amma dai manoman arewacin Sudan sai son barka, inda suka samu nasarar yin girbi baki daya.
A Karima, garin da ke gaɓa da kogin Nil kuma yake da nisan mil 210 daga babban birnin Khartoum - an fara girbin tare da matasa da ke hawa bishiyoyi suna karkado shi kasa, kan fararen ƙyallaye da aka shimfida.
Manoman da suke dogaro kan dabino na fuskantar matsalar kai shi zuwa sauran sassa na kasar, kamar dai yadda masu noma sauran kayayyaki ke fuskanta.
Tare da rashin tsaro, ƙarancin man fetur da yaki ya janyo ya sanya ba a iya kai kayayyakin inda ake so.
Kafin a fara yaƙin, kusan dukkan kasuwanci na waje guda a Sudan, a Khartoum.
Amma yawaitar harba bama-bamai da musayar wuta suka sanya babban birnin zama tsit babu 'yan kasuwa, wadand asuke tsoron lafiyarsu, ko wadanda mayakan suka kora a cibiyoyin binciken ababan hawa.
"Babbar kasuwarmu ita ce Khartoum," in ji Badawi. Idan babu wannan kasuwa, to farashin wannan amfanin gona zai yi ta karyewa.
An bar gonaki sun zama gayauna
A Sudan, dabino da sauran kayan amfanin gona sun kasance tushen tattalin arziki kafin a fara yaƙi a kasar.
Bangaren noma ne ke samar da kaso 80 na ayyukan yi a Sudan, kuma yana samar da kaso 35 zuwa 40 na kudaden da kasar ke samu a cikin gida, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Amma yanzu, a mafi yawancin yankunan kasar, ciki har da kudu maso-gabas na jihar Gedaref, wadda aka sani da zama kwandon kayan abincin Sudan, an bar gonaki sun zama gayauna.
An afka wa kamfanoni tare da sace kayayyaki.
Kananan manoma ba sa samun kudade, 'yan kasuwa ba su da tabbacin samun masu saye, kuma manyan attajirai ma sun fitar da rai.
A watan Mayu, Kungiyar Haggar -- daya daga cikin mafi daukar ma'aikata manoma -- ta dakatar da ayyuka tare da sallamar dubunnan ma'aikata.
Tun ma kafin a fara yakin, daya daga cikin mutane uku na cikin bukatar taimakaon jin kai -- kuma manoman kasar ba sa iya samar da dukkan abincin da ake bukata a kasar -- suna gwagwarmayar samar da abinci.
Sashen noman dabino a Karima na bukatar agajin gaggawa na neman mafita da tsare-tsare, da kuma dabarun yadda za a hana yin asarar dabinon, in ji wani manomi Al-Jarah ahmed Ali mai shekara 45.
A yanzu lamarin ya kara munana
Tun 15 ga watan Afrilu, aka fara rikici tsakanin bangaren Shugaban Rundunar Sojin Sudan Abdel Fattan Al Burhan da sashen tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, kwamandan mayakan RSF, wanda hakan ya kacalcala kasar Sudan.
Rikicin ya yi ajalin kusan mutum 7,500, kamar yadda Alkaluman Kungiyar Bibiyar Wuraren da Ake Yaki ta fitar.
Sama da mutum miliyan 4.2 -- mafi yawansu daga Khartoum -- sun rasa matsugunansu a Sudan, kuma wasu miliyan 1.1 sun gudu sun bar kasar, kamar yadda Kungiyar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Kasa da Kasa ta sanar.
Ma'aikata a gonaki na daga cikin masu guduwa su bar kasar, a yayin da suke samun nutsuwa a arewacin Sudan. Shin ko za su iya samun isassun kudade daga kasuwar dabino da ta tabarbare?
Daga cikin su akwai Hozaifa Youssef, mai shekara 26 da ke karatun likitanci ya bar Khartoum zuwa wajen iyalansa a Karima, inda yake taimakon su wajen girbe dabino.
Youssef ya ce "Ina kan hanya ta zuwa Indiya don karatun digiri na biyu," amma a yanzu wannan buri ya sha ruwa.
Babban manomi, Badawi bai fitar da rai ba.
"Muna kokarin neman sabbin masu sayen dabino, duk da cewa zai yi tsada. Muna sa ran farashin zai daidaita, kuma ya koma daidai.