Kamfanin rabbara wutar lantarki a Nijeriya (TCN) ya ce ya soma aikin gyara a layin tasharsa da ya gano ya samu matsala, wanda ya yi sanadiyar katsewar wuta a wasu sassan ƙasar.
Lamarin ya auku ne tun daga ranar Litinin 21 ga watan Oktoba kana ya shafi yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma wasu sassan yankin Arewa ta tsakiya a Nijeriya inda duk suka kasance cikin duhu.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar sashin hulda da jama'a na Kamfanin TCN Ndidi Mbah ta ce, tun daga ranar da aka samu katsewar wutar, tawagar ma'aikatan kamfanin suke ta koƙarin neman inda matsalar take amma ba su yi ''sa'a ba'' sai a yammacin ranar Laraba.
"Layin wutar da ya samu matsala ya kai tsawon inch 9, kuma karfinsa ya kai Kilowatt 330 wanda ke hanyar tashar wuta a fadamar dajin Igumale da ke jihar Benue.'' a cewar sanarwar da Kamfanin TCN ya wallafa a shafinsa na X.
"Bayan gano inda matsalar take, a yammacin ranar Laraba, tuni aka soma shirye-shiryen aika kayayyakin aiki zuwa wurin da lamarin ya faru don baiwa TCN damar fara ayyukan gyara,''a cewar sanarwar.
''Sakamakon yanayin wurin da matsalar ta faru, TCN na bukatar aika manyan motocin tono da ɗibar yashi da sauran kayan aiki daga ofishinsa na yankin Enugu zuwa inda lamarin ya faru domin soma aikin gyara." kamar yadda sanarwar ta yi kari akai.
Wannan dai shi ne karo na shida da ake samun irin wannan matsala da kan janyo katsewar wuta a tsarin lantarkin Nijeriya a cikin wannan shekara.
Kazalika yanayin na zuwa ne a daidai lokacin da aka kara kuɗin wutar lantarki a kasar a cikin watan Afrilu da kashi 240 cikin 100, wanda ya kara dagula wahalhalun da ' yan ƙasar ke fuskanta.