Lula ya yi ta nanata ‘Brazil ta dawo’, a yayin da ya ziyarci Shanghai /Hoto: Reuters

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki irin yadda dalar Amurka ta yi kaka gida a tattalin arzikin duniya tare da mamaye komai a Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF, a yayin wata ziyara da ya kai China.

“Me ya sa kowacce kasa za ta zama makale da dalar Amurka wajen gudanar da kasuwanci?” Tambayar da Shugaban Kasar barazil Lula ya yi kenan a wajen bikin kaddamar da kawarsa a siyasa Dilma Rousseff a matsayin shugabar bankin ci gaba na kungiyar kasashe biyar ta Brics [Brazil, Russia, India, China and South Africa], da aka yi a birnin Shanghai.

"Me ya sa bankin irin na kungiyar BRICS ba zai samar da kudinsa da zai dinga harkokin kasuwanci a tsakanin mambobin kasashensa ba? A yau kasashe ba su da zabi sai neman samun dala idan za su fitar da kaya waje, yaushe za su fara dogara da nasu kudaden?

Lula ya kuma yi suka da babbar murya ga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), inda ya ce Asusun na kakaba wa kasashe irin makwabciyarsa Barazil ka’idojin rage kasha kudade kafin a ba su basussukan kubutar da su daga kangin tattalin arziki da suke ciki.”

Ya ce “Ba wani banki da ya kamata ya dinga shake tattalin arzikin kasashen duniya kamar yadda IMF ke yi a yanzu ga Ajantina, ko kuma yadda suka yi wa Brazil tsawon lokaci.”

“Ba wani shugaba da zai yi wasa da wuka a makogoronsa saboda kasarsu ta ciyo bashi”.

‘Brazil ta dawo’

Lulu da ya kama aiki a watan Janairu na neman hanyar sauya fasalin Brazil a matakin kasa da kasa wajen mu’amala da kasashe tare da dawo da ita fagen daga ba kamar yadda aka mayar da ita saniyar ware a zamanin mulkin Jair Bolsanaro da ya gada ba.

Lula ya yi ta nanata ‘Brazil ta dawo’, a yayin da ya ziyarci Shanghai.

Lulu ya gana da shugaban China Xi Jinping a ranar Juma’ar nan inda suka tabo batutuwa da dama kan sha’anin siyasa da tattalin arzikin duniya.

Haka zalika sun tabo batun rikicin Yukren da Rasha. Kasashen biyu sun ki bin sawun kasashen Yamma wajen kakaba wa Rasha takunkumai.

TRT World