a a daidaita ƙimar musayar kudin na tsawon lokacin wannan ciniki in ji Fadar Shugaban Kasa.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya bai wa kamfanin mai na ƙasar NNPC umarnin ya dinga sayar wa matatar fetur ta Dangote ɗanyen mai a Naira maimakon dalar Amurka.

Hakan na ƙunshe ne a sanarwar da mai taimaka wa Shugaban Ƙasar kan watsa labarai da tsara dabaru Bayo Onanuga ya wallafa a shafina na X a ranar Litinin.

“Domin tabbatar da daidaiton farashin man fetur da kuma farashin Dala da Naira, a yau Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da ƙudirin da Shugaba Tinubu ya gabatar na sayar da ɗanyen mai ga Matatar Dangote da sauran matatun mai da ke tafe a kan farashin Naira,” in ji sanarwar.

Wannan lamari na zuwa ne bayan da ake dinga samun takun-saƙa a ‘yan makonnin nan tsakanin mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kuma shugaban kamfanonin rukunonin Dangote, Aliko Dangote da gwamnatin Nijeriya a kan batun matatar man tasa da ke Legas.

Matatar Dangote a halin yanzu tana buƙatar sunduƙan dakon kaya 15 na ɗanyen mai, a kan kudi dala biliyan 13.5 duk shekara, inda kamfanin NNPC ya ƙuduri aniyar samar da guda huɗu.

Sai dai a cewar sanarwar, hukumar ta FEC ta amince da cewa ganga 450,000 da za a yi amfani da su a cikin gida za a ba da su a kan farashin Naira ga matatun man Nijeriya, ta hanyar amfani da matatar Dangote a matsayin gwaji. Za a daidaita ƙimar musanya na tsawon lokacin wannan ciniki.

Bankin Afirka na shigar da fitar da kayayyaki Afrexim da sauran bankunan Nijeriya ne za su saukaka kasuwanci tsakanin Dangote da Kamfanin NNPC. Wannan shiga tsakanin zai kawar da buƙatarneman bashi na ƙasa da ƙasa, tare da ƙara ceton ƙasar daga biyan kuɗi a kan dala.

TRT Afrika