Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Elon Musk a Gidan Turkiyya gabanin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na 78da za a yi a New York. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da shugaban kamfanin kera motoci na Tesla Elon Musk a New York, inda ya gayyace shi Turkiyya sannan ya nemi ya bude reshen kamfanin na bakwai a kasar.

Lokacin ganawarsu, wadda suka yi a Gidan Turkiyya wato (Turkevi Center) a Manhattan, Erdogan ya shaida wa Musk, mai kamfanonin Tesla da SpaceX, ci-gaban da "Turkiyya ta samu a fannin fasaha da kuma shirinmu mai suna ‘Digital Türkiye’ da ke mayar da hankali kan bunkasar fasaha da tsarin Kasa na Kikirarriyar Basira wato National Artificial Intelligence Strategy," a cewar Daraktan Sadarwa na Turkiyya a sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta kara da cewa Erdogan ya gaya wa Musk yadda motar Togg mai amfani da lantarki da Turkiyya ta kera ta karbu a kasuwa yana mai cewa bude reshen Tesla a kasar zai habaka wannan fanni.

"Shugaba Erdogan ya kara da cewa za a samu damar hada gwiwa da kamfanin SpaceX ta hanyar matakan da za a dauka sannan zai kasance wani bangare na shirin Turkiyya na zuwa sararin samaniya inda ya gayyaci Musk ya halarci baje-kolin harkokin fasaha mai suna Teknofest wanda za a yi a Izmir," a cewar sanarwar.

Sanarwar Daraktan Sadarwa na Turkiyya ta ce Musk ya bayyana cewa tuni wasu Turkawa da ke kera kayayyaki suke aiki da Tesla kuma Turkiyya na cikin kasashen da yake son bude rassan kamfanin nasa.

A martanin da ya mayar kan batun tayin da Shugaba Erdogan ya yi kan hadin kai da kamfanin tauraron dan adam na Starlink mallakar SpaceX, Musk ya bayyana cewa suna so su yi aiki da hukumomin Turkiyya domin samun lasisin da ya kamata don samar da sabis din Starlink a Turkiyya.

A lokacin tattaunawar, Mista Erdogan ya kuma bayyana irin nasarar da Turkiyya ta samu wurin kera jirgi mara matuki na Bayraktar TB2, inda Musk ya ce yana sane da yadda duniya ke nuna sha’awa kan jirage marasa matuka, in ji sanarwar.

Erdogan ya ba Elon Musk littattafai biyu

Bayan tattaunawar, an ga Musk da littattafai biyu, "A Fairer World is Possible" da kuma "UN Reform: A New Approach to International Cooperation" wadanda Erdogan ya ba shi. A duka kafofin duniya, an san Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na tsawon lokaci da son ganin an yi adalci a duniya.

Littafin nasa na "A Fairer World is Possible", ya kasance wata shaida wadda ta nuna yadda Shugaba Erdogan ke son ganin an yi adalci a duniya musamman ga wadanda aka zalunta.

Erdogan na ganin yadda tsarin Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya yake na daga cikin dalilan da suka sa ake samun rashin adalci a fadin duniya.

Mambobi biyar na dindindin a Majalisar sun hada da kasashe daga nahiyoyin Asia da Turai da Amurka amma babu wata kasa daga Afirka, kamar yadda Erdogan ya rubuta.

Littafin na biyu mai suna "UN Reform: A New Approach to International Cooperation" na bayani ne kan dalilin da ya sa Turkiyya ke son ganin an samu sauyi a Majalisar Dinkin Duniya da Majalisar Tsaronta.

Littafin wanda aka wallafa shi da Turkanci da kuma Ingilishi, ya yi bayani kan yadda Majalisar Dinkin Duniya da Majalisar Tsaro wadanda aka kafa bayan Yakin Duniya na biyu, suka kasa samar da wata mafita kan matsalolin da ake fama da su a yanzu.

Littafin na dauke da bangarori uku: Me ya sa ake bukatar sauyi a MDD? Sai kuma ‘Amfanin Majalisar Dinkin Duniya wurin samar da zaman lafiya a duniya da magance matsalolin bi ladama,’ sai kuma ‘dalilan sauyi a MDD da shawarwari.’

TRT World