Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta ce za ta ladabtar da kamfanin tauraron ɗan'adam na Starlink mallakin Elon Musk, sakamakon ƙarin kuɗaɗe ga masu amfani da shi a ƙasar ba tare da samun amincewarta ba.
An bayyana haka ne a wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama'a na Hukumar Reuben Muoka ya fitar a ranar Talata.
A wani saƙo da aka aike wa kwastomomi a makon da ya gabata, Starlink ya ce ƙarin kuɗaɗen da yake caja zai shafi sabbi da tsoffin kwastomominsa.
An ƙara kuɗin amfani da Starlink da kashi 96, daga Naira 38,000 zuwa 75,000.
Kazalika, sabbin masu amfani da Starlink za su biya kuɗi mai yawa na na'urar da ake sakawa don fara amfani da tauraron ɗan'adam ɗin, wanda yanzu ya kai Naira 590,000, ƙarin kashi 34 fiye da yadda yake a baya kan N440,000.
Sai dai kuma, NCC ta sanar da cewa ba ta amince da a yi wannan ƙari ba.
Muoka ya ce "Wannan mataki na Starlink ne na ƙashin kansa don ƙara kuɗaɗen da suke caja, kuma bai samu amincewar Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ba."
Ya ƙara da cewa hukumar ta yi "mamaki" a lokacin da kamfanin ya sanar da ƙara farashin, duk da cewa ya shigar da buƙatar neman hakan ga NCC.
A cewarsa, kamfanin ya saɓa wa sashe na 108 da 111 na Dokar Sadarwa ta Nijeriya (NCA) ta 2003, da kuma sharuɗɗan lasisin Starlink game da ƙayyade farashi.
"Hukumar za ta ɗauki matakan da suka kamata don ƙalubalantar duk wani da ya yi karan-tsaye ga dokokon ma'aikatar sadarwar."
Sashe na 108 da 111 na NCA 2003 sun bai wa Hukumar NCC damar saka dokoki game da kuɗaɗen da kamfanonin sadarwa za su caji kwastomomi, inda dokar ta bayyana cewa babu wani da aka baiwa lasisi da ke da ikon ƙayyade farashi ba tare da amincewar hukumar ba.
Kazalika, sashe na 111 ya bai wa NCC damar cin tara ga duk wani kamfani da ya caji kuɗaɗe sama da yadda hukumar ta amince ya karɓa, ba tare da duba ga wasu ƙa'idojin shari'a ba.