Kasashen Gana da Ivory Coast ne suke samar da akalla kashi 60 na kokon da ake samarwa a duniya/ Hoto: Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

“Ghana da Ivory Coast ke samar da kashi 65 cikin 100 na koko a duniya, amma kashi 6 cikin 100 na kudin da ake samu daga kokon ne ke isa ga manoma”.

Wannan ne sakon da mataimakin shugaban kasar Ghana, Mahamudu Bawumia, ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan da aka kafa kungiyar CIGCI ta kare muradun manoma da kasashe masu noman koko.

Samar da riba mai tsoka ga manoman koko na daya daga cikin manufofin kungiyar ta CIGCI, kuma tuni kungiyar , wadda ke da hedikwata a Ghana, ta kama aiki kan ganin ta cimma manufofinta.

Har ma wasu rahotanni sun ce kasashe irin su Nijeriya da Kamaru suna son hada kai da kungiyar ta CIGCI domin su ma manomansu su fara amfana da tsarin kungiyar wanda zai kara musu kudin shiga.

Shin wannan tsari ne mai dorewa?

Tun da aka fara wannan tsarin ne wasu suka fara hasashen cewar tsarin ba zai dore ba, suna cewa zai iya sa farashin cakulan ya kara tashi.

A ganinsu, lamarin zai rage cinikin masu yin cakulan din tare da rage bukatar kokon da ake amfani da shi wajen sarrafa cakulan.

Amman ba kowa yake da wannan ra’ayin ba, wasu na ganin kafa kungiyar CIGCI mafita ce ga kasashe masu noman koko.

Manufofin CIGCI sun hada da nema wa manoma koko kudin shiga mai tsoka/ Hoto: Reuters

“Tsarin CIGCI tsari ne mai dorewa idan har kasashen biyun da suka fi noman koko za su ci gaba da aiki tare don jin dadin manomansu,” kamar yadda Philip Abayori, shugaban cibiyar cinikayyar kayayyakin gona ta Ghana, ya shaida wa TRT Afrika.

Ya ce idan aka kwatanta dalar Amurka biliyan 32 da ake samu bayan an sarrafa kokon, da abin da kasashen biyu da manomansu ke samu, za a ga babu laifi idan an kayyade wani kudi kan kokon.

A ganinsa wannan zai kawo ci gaban fannin noma cikin kankanen lokaci ta hanyar inganta himmar aiki da kuma samar da aikin yi ga jama’a baki daya.

Me ilimin tattalin arziki ke cewa game da kayyade farashi?

Kungiyar CIGCI ta ce a kowace shekara farashin koko ke faduwa, lamarin da ke talauta manoma kafin a kafa kungiyar/ Hoto: Reuters

“Idan har abin da ake son a kafa shi ne kungiyar masu noman koko, idan manomanmu na noma koko da yawa, me za mu yi da kokon,” in ji Dr Patrick Opoku Asuming, malami a fannin nazarin kasuwanci na Jami’ar Ghana.

Ya ce: “Za mu ajiye kokon a kasashenmu ne don muna son farashin kokon ya tashi? Ba na ganin wannan tsari ne mai dorewa.”

A ganinsa ya kamata kasashen su mayar da hankali kan yadda za su sarrafa kokon ta yadda za su kara samun kudi maimakon sayar da danyen kokon yadda suke yi a yanzu.

“Ina ganin tsarin kasuwanci mara shinge a fadin Afirka (EFCFTA) wata dama ce ta sayar wa mutane masu yawa kokon da aka sarrafa,” a cewar Dr Patrik.

Idan aka kara samun sabbin hanyoyin amfanin da kokon, za a iya kauce wa matsalar da ka iya tasowa idan kasashen duniya masu sayen kokon suka daina sayensa bayan sun maye gurbinsa da wani abu wajen hada koko.

Duk da cewa an fi cin cakulan a duniya yanzu fiye da da, manoma koko na fama da talauci /Hoto:Reuters

Sarrafa koko a gida

Sarrafa koko a gida wani abu ne da aka dade ana magana a kansa. Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, ya taba cewa Ghana za ta daina fitar da danyen koko kasashen waje.

“Ghana ba ta son ta ci gaba da dogaro kan samar da tare da fitar da kayayyakin da za a sarrafa ciki har da koko,” a cewar shugaban kasar na Ghana a wani taro da aka yi a Majlisar Dokokin Switzerland a birnin Bern a shekarun baya.

“Muna so mu rinka kara yawan kokon da muke sarafawa zuwa cakulan da kanmu don mun yi imanin cewar mutanen Ghana ba za su sami wadata ba idan mun dogara kan fitar da kayayyakin da ba a sarrafa ba,” in ji shi.

Kasashen Turai da Amurka sun fi samun kudi kan koko fiye da kasashen yammacin Afirka da suka fi noman kokon /Hoto:Reuters

Kalubalen sarrafa koko a gida

Sai dai tun da shugaban ya yi wannan maganar, har kawo yanzu kasar ba ta daina fitar da kokon da ba a sarrafa ba.

Daya daga cikin abubuwan da ke hana sarrafa cakulan a kasar ta Ghana da ma yammacin Afirka shi ne rashin ishasshiyar madara. Madara wata sinadari ce mai muhimmanci wajen hada cakulan.

Har yanzu ana shigowa da mafi yawa daga cikin madarar da ake amfani da ita a yankin daga ketare.

Wata matsalar kuma ita ce yanayi na zafi da ake da shi a yankin. Idan zafi ya yi yawa yakan narkar da cakulan.

Rashin wutar lantarki mai dorewa na daya daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga sarrafa koko zuwa cakulan.

Duk da haka, ana samun kamfanoni masu sarrafa kokon a kasar Ghana.

Sai dai wannan bai sa kasar tana samun kaso mai tsoka ba daga kudin da ake samu bayan an sarrafa kokon.

Wadanda suke kokarin sarrafa koko a Ghana suna fuskantar kalubale da yawa /Hoto: Reuters
TRT Afrika