Sanye da tufafinta na ranar Lahadi cikin farin ciki, Sonia Chukwu, wacce ta kammala karatun digirinta na farko a jami'a, ta yi ta daukar hotuna da dama ita da kawayenta da wayarta.
Cikin 'yan mintoci kadan, ta dora hotunan a kafar Facebook, kuma a cikin kasa da sa'a guda, ta samu sama da 'likes' 100 daga abokanta da ke bin ta a kafar, Ga Sonia, burinta ya cika na wannan rana.
A ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairu ne kamfanin kafar Facebook ya cika shekaru 20 bayan da Mark Zuckerberg dalibi mai karatun digiri na biyu a Jami’ar Harvard ya kirkiro shi tare da abokansa su uku a cikin wani dakin kwana na dalibai.
Kamar Sonia, Facebook ya zama dandalin da ya wuce wurin haduwa da abokai kawai.
''Facebook shi ne wurin da ke kubutar da ni daga shiga damuwa; yana cetona a duk lokacin da na fada cikin wani yanayi.
A wurin da nake gani da kuma saduwa da mutane da suke faranta min rai, kuma da gaske, abun da na damu da shi kenan kawai,’’ kamar yadda Sonia ta shaida wa TRT Afrika.
"A tsawon shekarun da suka gabata, kafar Facebook ta sauya daga hada tsofaffin abokai da sababbi zuwa wani dandali da ke karfafa masu kirkirar shirye-shirye wajen ba su kyauta ta hanyar kara wa rayuwarsu armashi,'' in ji Uche Aitkins wani mazaunin jihar Legas na Nijeriya da ya fice wajen amfani da kafar.
Facebook na da mabiya fiye da mutum biliyan biyu wadanda suke amfani da kafar a kullum sannan 'yan Afirka kusan mutum miliyan 271 suke amfani da kafar.
Ana hasashen adadin zai kai sama da miliyan 377 nan da shekarar 2025, a cewar dandalin bincike na Statista.
A shekarar 2004, Facebook ya kasance shafin Harvard ne kawai.
Bayan wasu watanni da shekaru kafar ya bunkasa inda ya fara ba da dama ga dalibai daga wasu kwalejoji da jami'o'i su yi rajista, sai kuma manyan makarantun sakandare da kwararru da adireshin imel na kamfanoni.
A shekara ta 2006, yawancin wadanda suka fara mafani da kafar sun tsufa daga alkalumansu shekarunsu na asali, hakan ya sa Facebook ya kaddamar da wasu karin hanyoyin rejistan zama memba na kafar.
"Muna da shekara biyu na tsofaffin dalibai, kuma fiye da kashi daya bisa uku na mutanen da ke amfani da shafin sun kammala karatunsu a jami'a,'' in ji Zuckerberg a yayin hirarsa da New York Times a 2006, daga wannan lokacin ne shafin ya bude kofofinsa ga duk wanda ya wuce shekaru 13.
"Idan muka sanya shi ta yadda sauran matasa za su iya amfani da shafin, hakan zai karfafa gwiwar kowa da kowa," in ji wanda ya kafa Facebook.
Mutane da dama za su ce Zuckerberg ya cika alkawarinsa la'akari da yadda dandalin ke karafafa kwarewar mai amfani, musammam ta hanyar kaddamar da ilimin fasaha na (AI).
Ga Ifeanyi Ewuzie, wani mai sana'ar sayar da kaya, a zahiri Facebook ya taimaka masa wajen samun ci gaba a kasuwancinsa.
"A matsayina na ɗan kasuwa, Facebook yana samar mun da mutanen da zan tallata wa hajata, sannan yana taimaka min wajen habaka kasuwancina da kuma hulda kai tsaye da abokan cikinina," kamar yadda Ifeanyi ya shaida wa TRT Afrika.
A shekarar 2021, Facebook ya sanar da sabon sunan kamfaninsa mai dauke da sauran kafofin sada zumunta, inda ya saka masa suna 'Meta' don kara nuna burin ci gaban kamfanin.
Meta ya kara wa dandalin armashi wajen shigar da fasahar AI, wadda masu mafani kamar Ifeanyi suka ce ta taimaka wa nasarar kasuwancinsu.
''Facebook yana da ikon taimaka min wajen gina ko habaka abokan cinikina na kasuwanci. Kazalika, Facebook yana bai wa mutum damar yin nazari ko daukar matakai masu muhimmanci don bin diddigi da auna ayyukan kasuwancinsa a shafinsa na kafar, wanda hakan ya ba ni damar daidaita dabarun tallata hajata bisa ga bayanan masu amfani,'' in ji Ifeanyi.
Duk wannan ci gaba, Facebook ya yi ta fama da cin zarafi da batutuwan da suka shafi bayanai na tsaro da take ka'idojin kasuwanci, da kuma suka da ke da alaka da hakkin fadin albarkacin baki.
A watan Mayun 2023, aka ci tarar wanda da ya kirkiro Facebook da Meta dala biliyan 1.2 (£1bn) kuma aka ba shi umarnin ya dakatar da canja wurin bayanan masu amfani na kasashe kungiyar EU zuwa Amurka.
A watan Agustan 2022, Facebook ya sanar da cewa yana gudanar da bincike kan wata matsalar tsaro da ta shafi masu amfani da kafar sama da mutum miliyan 50.
Duk da haka, tasirin Facebook a rayuwar al'umma na ci gaba da bunkasa a mastayin kafar wacce ta yi shura tsakanin sauran kafofin sada zumunta na intanet.