Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta yi asarar sama da Naira Tiriliyan 4.3 na danyen mai ta hanyar satar man sakamakon fasa bututai guda 7,143 a cikin shekara biyar.
An bayyana wannan adadi mai ban mamaki ne a wajen Taron Fasaha da Tsaro na Kasa da Kasa na Nijeriya da aka gudanar a Abuja, inda aka bayyana irin illar da satar man fetur ke yi ga tattalin arzikin kasar.
A wani jawabi da hukumar da ke tabbatar da cewa masana’antun da ke haƙo ma’adinai na aiki bisa gaskiya, (NEITI) ta gabatar a wajen taron, ta zayyana mummunan halin da ake ciki na satar man fetur, inda ta ayyana shi a matsayin "aikin gaggawa na kasa."
Shugaban hukumar NEITI, Ogbonnaya Orji, ya jaddada babbar illar satar ɗanyen fetur, da illar da yake haifarwa wajen haƙo mai, da cin hanci da rashawa, da daƙile bunƙasar tattalin arziki da kasuwanci da kuma ribar kamfanonin mai.
Orji ya bayar da bayanai masu ban mamaki daga rahotannin NEITI, inda ya bayyana cewa a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, Nijeriya ta samu rahoton fasa bututun mai guda 7,143 da kuma fasa bututun mai da gangan.
Hakan ya yi sanadin satar ganga miliyan 208.639 na danyen mai da darajarsa ta kai dala miliyan 12.74 kwatankwacin Naira tiriliyan 4.325.
Bugu da ƙari, Orji ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci, Nijeriya ta kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 471.493 don gyaran ko kula da bututan mai da suka lalace.