Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da ke yankin kudancin Nijeriya ya bayyana takaicinsa game da koma bayan da jiharsa ta samu daga matsayinta na ɗaya a cikin jihohi masu arzikin masana’antu da wuraren da aka fi son zuba jari a cikin gida da wajen Nijeriya.
A yayin jawabinsa a wajen buɗe taron koli na tattalin arziki da zuba jari na kwanaki biyu a babban birnin jihar Fatakwal a ranar Laraba, Fubara ya danganta matsalar da ''ƙarancin ci gaban tattalin arziki da ƙarancin kuɗaɗen haraji da yawan rashin ayyukan yi da jinkirain samar da ci gaba.''
Taron, kan zuba jari irinsa na farko an yi masa take da, "Rivers Emerge: Advancing Pathways to Growth Economic and Sustainability." wato Ribas ta hallara: Bunƙasa Hanyoyi zuwa ga Ci Gaban Tattalin Arziki da Ɗorewarsa.''
Gwamnan ya yi waiwaye kan lokacin da jiharsa musamman birnin Fatakwal da aka kafa amatsayin cibiyar kasuwanci a Nijeriya ke samar da ci gaba, yana mai nuni da hanyar masana'antar Trans-Amadi da ke tsakiyar birnin, wacce ta haɗa kasuwanci da masana'antu da dama waɗanda suka samar da ayyukan yi ga al'ummar jihar da kuma kuɗaɗen shiga.
Sai dai a wani saƙo da Fubura ya wallafa a shafin na X kan taron ya bayyana cewa ''An fara aikin maido da martabar jihar Ribas ta fuskar tattalin arziki ga masu zuba jari na gida da na waje''.
Yana mai kari da cewa za a fitar da sabbin damammaki da dabaru da za su karfafa gwiwa bayan taron koli na tattalin arziki da zuba jari na jihar Ribas.
''A shirye mu ke tsaf da don yin maraba da masu zuba jari a fannonin noma da man fetur da iskar gas da sarrafa kayan ayyukan noma da ƙarafa da dai sauran su don dawo da martabar masana’antu a jiharmu da kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi ga matasanmu masu tasowa,'' in ji gwamnan a shafinsa na X
A jawabinsa yayin taron, tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Sarkin Kano na 14 Khaifa Muhammadu Sanusi ya yi kira ga hukumomin Nijeriya su nemi wasu hanyoyin samar wa ƙasar kuɗin shiga.
Ya ce "Jihar Rivers ta yi sa'a tana da albarkar man fetur, kyautar da ta taimaka sosai wajen ba da gudunmuwa ga tattalin arzikin Nijeriya baki ɗaya. Amma wadata da arzikin man fetur bai isa ya kawo ci gaba tattalin arziki ba."