Kamfanin ya samu raguwa da kaso 24.7 cikin 100 a shekarar 2023 a ribar da ya samu. / Hoto: Getty Images

Kamfanin mai na Saudi Aramco ya sanar da samun raguwa a ribar da ya samu a shekarar 2023 idan aka kwatanta da shekarun baya.

A sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa ya samu raguwa da kaso 24.7 cikin 100 a 2023 kuma hakan ya samo asali ne sakamakon faɗuwar farashin man fetur da kuma rage haƙo man.

Saudi Aramco ya ce a shekarar 2022 ya samu ribar dala biliyan 161.07 amma a 2023 ya samu dala biliyan 121.25.

“Wannan raguwar ta fito da tasirin raguwar farashin ɗanyen mai da kuma raguwa a adadin da ake sayarwa,” kamar yadda kamfanin ya sanar.

Mamayewar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun 2022 ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi, inda ya kai sama da dala 130 kan kowace ganga a shekarar.

A rahoton da Aramco ya bayar ga gwamnatin ƙasar a 2022, ya ce riba ce ya samu mai tarihi sakamakon sai da ya bayar da rarar kuɗi a karon farko a kusan shekara goma.

Hawa da saukar farashin mai

Sai dai a bara, farashin mai ya ragu zuwa dala 85 a kowace ganga, wanda ya haifar da raguwa a ribar da ake samu.

Ana sa ran farashin zai tashi zuwa kusan dala 88 a kowace ganga a bana, sakamakon rashin tabbas a duniya saboda yakin Isra'ila da Hamas, in ji wani kamfani mai zaman kansa na Riyadh Jadwa Investment a wani rahoto da aka buga a watan Oktoba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Zai iya kaiwa dala 90 kan kowacce ganga a karshen shekarar 2024, in ji Jadwa Investment.

Ƙasar Saudiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi haƙo ɗanyen man fetur a duniya

AFP