A wata sanarwa ta ba-zata da manyan kasashen duniya da ke da arzikin hako mai na kungiyar OPEC karkashin jagorancin Saudiyya suka fitar, sun ce za su rage adadin man da suke hakowa da ganga sama da miliyan daya a ko wacce rana.
Sanarwar ta ce matakin yin hakan zai zama wani rigakafi ne da zai taimaka wajen daidaita kasuwannin man a duniya, duk kuwa da kiran da Amurka ta yi na cewa a kara yawan man da ake hakowa don dakile hauhawar farashin kayayyaki.
Sabon matakin da Saudiyya da Iraki da UAE da Kuwait da Aljeriya da kuma Oman za su dauka daga watan Mayu zuwa karshen shekar, zai zama mataki mafi girma da kungiyar OPEC da abokan huldarta suka dauka tun bayan rage hako gangar danyen mai miliyan biyu a kowacce rana da suka yi a watan Oktoba.
Rasha wadda ke daya daga cikin jagororin kungiyar ta OPEC ta bayyana cewa ita ma za ta ci gaba da rage yawan danyan man da take hakowa da a kowace rana da ganga 500,000 har zuwa karshen shekara, inda take kwatanta matakin a matsayin wani rigakafi da kuma abin da ya dace.
Farashin man ya yi tashin gwauron zabo da kusan kashi shida cikin 100i a kasuwannin kasashen Asiya a safiyar Litinin da kashi 5.74 cikin 100 zuwa dala 80.01 cikin 100 kan kowacce ganga.
Ita ma Amurka farashin kasuwar manta ya haura da kashi 5.67 cikin 100 zuwa dala 84.4.
''Wani jami'i a ma'aikatar makamashi ta Saudiyya, ya ce matakin na baya-bayan nan wani mataki ne na ‘’rigakafi’’ da zai taimaka wajen daidaita kasuwar man fetur,'' in ji kamfanin dillancin labaran Saudiyya.
Rage farashin man dai ya biyo bayan faduwar farashin danyen man wanda ya yi tasiri wajen durkushewar da wasu manyan bankunan Amurka suka yi.