Shugaban kamfanin mai na Nijeriya (NNPC) Mele Kiyari, ya ce za a cigaba da neman mai a kasar don bunkasa tattalin arziki

Kamfanin mai na Nijeriya NNPC na neman hanyoyin da zai dinga bayar da danyen man ga masu sarrafa shi a cikin gida, wadanda a yanzu suke ƙorafin wannan mataki zai iya jefa samuwar masu zuba jari cikin hatsari a bangaren sarrafawa da sayar da albarkatun man.

Tun bayan kaddamar da matatar mai ta Dangote da za ta dinga tace mai ganga 650,000 a kowacce rana a watan Mayu, ta zama kamar kango, tana jiran a kai mata ɗanyen mai, kuma dole a yanzu NNPC ya cika yarjejeniyar da aka kulla ko ya rasa mallakar kaso 20 na matatar.

Majiyoyi a Ma'aikatar Albarkatun Man Fetur da ke Abuja na cewa Nijeriya na fuskantar hatsarin gaza mallakar kaso ashirin na matatar Dangote, saboda gaza cika ka'idojin yarjejeniyar da aka kulla na mallakar wani bangare na matatar.

A karon farko, jaridar intanet ta BusinessDay ta yi kokarin rawaito cewa kason gwamnati a matatar ya kai dala biliyan 2.7, kuma an shirya gwamnatin tarayya za ta biya don mallakar kaso 20.

An amince da tsarin biyan kudaden, za a biya tsabar kudi da kuma kai wa matatar man ɗanyen mai.

NNPC ya ɓoye bayanai game da tsarin biyan kudaden, kuma bai taba bayyana wa 'yan Nijeriya yadda abun yake ba.

Baya ga biyan dala biliyan daya, an kuma amince NNPC zai kaiwa matatar Dangote danyen mai na dala biliyan daya, sannan zai biya sauran dala miliyan 700 daga ribar da zai samu daga matatar man.

A farkon watan nan an rawaito cewa kamfanin man zai kai wa matatar Dangote danyen mai a manyan jiragen ruwa da za a yi amfani da shi a matsayin gwaji a watan Disamba.

A jawabin da Dangote ya yi yayin kaddamar da matatar man a watan Mayu, ya bayyana cewa za ta biya bukatar mai ga Nijeriya da kasuwannin Afirka.

TRT Afrika da abokan hulda