Kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya ce wani kamfanin tsaro da ya dauki hayarsa ya kama jirgin ruwa dauke da danyen fetur na sata da ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Kamaru.
Wata sanarwa da kakakin NNPCL, Garba Deen Muhammad, ya fitar ranar Litinin ta ce kamfanin tsaron na Tantita Security Services ya kama jirgin ruwan, mai dauke da lita 800,000 na danyen fetur, ranar 7 ga watan Yuli bayan ya samu bayanan sirri game da shi.
Ya kara da cewa an kama kaftin da ma'aikatan jirgin ruwan na MT TURA II, mallakin wani kamfani da aka yi wa rajista a Nijeriya mai suna Holab Maritime Services.
"Binciken farko ya nuna cewa an samo danyen man fetur din ne ta haramtacciyar hanya daga wata rijiyar mai da ke jihar Ondo ta Nijeriya. Babu wata shaida ta hakika da ke nuna bayani game da jirgin ruwa da danyen man fetur din da ya dauko ya zuwa lokacin da aka kama shi," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa jirgin ruwan ya kwashe fiye da shekara 12 yana gudanar da irin wannan danyen aiki a Nijeriya.
A cewar NNPCL, an yi wa hukumomin da suka dace bayani game da kama jirgin ruwa da kuma sakamakon binciken da aka gudanar a kansa, kuma an amince a lalata shi domin zama izina ga masu satar danyen fetur.
"Lalata jiragen ruwa da ke dauke da danyen man fetur na sata yana da matukar muhimmanci a matsayin hanyar hana sake aukuwar hakan,"in ji sanarwar.