A yau Juma’a ne matatar mai ta Dangote da ke Nijeriya za ta karɓi danyen mai karo na farko, har ganga miliyan daya daga kamfanin mai na Shell, lamarin da zai jawo matatar ta fara aiki gadan-gadan bayan shafe shekaru ana jinkiri.
Da zarar an kammala aiki, matatar man, wadda hamshakin attajirin Afirka Aliko Dangote ya gina, tana da ƙarfin dinga samar da ganga 650,000 a kowace rana, lamarin da zai mayar da Nijeriya mai arzikin fitar da man fetur, abin da kungiyar ta OPEC ta daɗe tana fata, bayan da a yanzu kusan ta dogara ne da shigar da tataccen fetur daga kasashen waje.
Kamfanin Dangote ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani a ranar Juma’a, inda ya ce jigilar gangar danyen mai samfurin Agbami miliyan daya da ta saya shi ne na farko cikin ganga miliyan shida da za a fara gudanar da aiki da shi a matatar.
Hakan zai sa a fara fitar da man dizal da man jirgin sama da iskar gas, kafin daga baya matatar ta fara samar da man fetur na amfanin motoci.
Mai magana da yawun kamfanin Dangote ya ce ana sa ran jirgin ruwan dakon kaya na STASCO zai isa matatar man a yau Juma’a.
Kamfanin mai na Nijeriya NNPC ne zai kai jiragen ruwan dakon guda hudu nan da makonni biyu zuwa uku sannan kuma jirgin ruwan dakon na karshe zai fito ne daga ExxonMobil, in ji kamfanin Dangote.
Duk da kasancewar Nijeriya kasa mafi arzikin man fetur a Afirka, amma tana fama da karancin man fetur akai-akai.
A shekarar da ta gabata Nijeriya ta kashe dala biliyan 23.3 wajen shigo da man fetur daga kasashen waje kuma ana amfani da kusan lita miliyan 33 na mai a rana a ƙasar.
"Babban abin da muka mayar da hankali a kai a watanni masu zuwa shi ne bunkasa matatar ta yadda za ta iya,” in ji kamfanin Dangote a cikin sanarwar.
A watan Mayu ne Nijeriya ta ƙaddamar da matatar man, bayan da aka ɓata tsawon lokaci ba a yi hakan ba. Matatar wacce aka gina ta a kan kudi dala biliyan 19, na daya daga cikin manyan jarin da Nijeriya ta taɓa zubawa.