Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) ya kaddamar da cibiyar sa ido kan ayyukan samar da man fetur (PMCC), wanda ya zama wani shiri na bunkasa ayyukansa wajen samar da fetur iskar gas a ƙasar.
Shirin, wanda kamfanin NNPC Upstream Investment Management Services (NUIMS) ke jagoranta, ya ginu ne a kan nasarar da Cibiyar Kula da Umarni ta samu don inganta sa ido da gudanar da ingantaccen aiki, da kuma samar da man fetur.
Sanarwar da NNPC ya wallafa ranar Laraba a shafinsa na X ta ce Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce tsarin PMCC ya yi daidai da manufofin Shugaba Bola Tinubu na haɓaka inganci da samar da albarkatu a masana'antar fetur.
“PMCC yana aiki ne a matsayin wani dandali na haɗin gwiwa don sa ido kan dangogin fetur tun daga samarwa zuwa fitar da su da ma rarraba su.
"Ta hanyar haɓaka bayanan da ke nuna yadda komai ke tafiya kai tsaye, PMCC zai dinga ba da cikakken bayani game da ayyukan yadda ake samarwa.
"Wannan zai sa a dinga gano ayyuka marasa kyau da ke faruwa a kan lokaci da kuma daƙile rushewar sashen da ma yin komai babu ƙumbiya-ƙumbiya.
"Tare da nazarce-nazarce na ci gaba da kuma bayanan da aka haɗa, PMCC zai dinga ƙarfafa wa masu ruwa da tsaki da kuma ba su cikakkun bayanai don fahimtar aiki musamman a lokutan da suke son ɗaukar matakai,” ya ce.
Ya kara da cewa, PMCC na inganta hadin gwiwa a tsakanin masu ruwa da tsaki ta hanyar samar da ingantaccen tsari don musayar bayanai da sadarwa da samar da ingantacciyar hanyar warware matsaloli da kuma samar da ci gaba a fadin fannin.
Ya ce rawar da PMCC zai taka wajen tabbatar da inganta injina da gyaransu zai ba da gudunmawa kai tsaye ga karuwar samarwa da kudaden shiga.