Dele Alake gwamnatin Nijeriya ta soke lasisin kamfanonin ne a yunkurin da take yi na tsaftace fannin hakar ma'adinai domin ya dace da tsarin kasashen duniya.

Gwamnatin Nijeriya ta soke lasisin kamfanoni 1,633 masu hakar ma’adinai saboda rashin biyan haraji na shekara-shekara, kamar yadda Ministan Harkokin Ma’adinai ya bayyana ranar Talata.

Kamfanonin, wadanda ke cikin kamfanoni 2,213 da gwamnatin kasar ta zayyana domin kwace lasisinsu, sun hada da kamfanoni masu duba ingancin kasa 536, da kamfanoni 279 da ke hakar ma’adinai, da kamfanoni 787 da su ma suke hakar ma’adinai amma mara yawa, da kuma kamfanoni 31 da aka ba su hayar hakar ma’adinai, in ji Minista Dele Alake ko da yake bai bayyana sunayensu ba.

An soke lasisin ne bisa umarnin dokar Nijeriya wadda ta bukaci masu rike da lasisin su rika biyan haraji na shekara-shekara, ko kuma a soke lasisinsu.

Mr Alake ya ce kamfanoni 580 ne kawai suka biya harajin da ake binsu na shekara-shekara bayan an ba su wa’adin kwana 30 domin yin hakan. Wa’adin ya kare ne ranar 10 ga watan Nuwamba.

Ya kara da cewa gwamnati ta soke lasisin kamfanonin ne a yunkurin da take yi na tsaftace fannin hakar ma'adinai domin ya dace da tsarin kasashen duniya.

Nijeriya tana kokarin jawo hankali 'yan kasuwar kasashen waje domin zuba jari a fannin hakar ma'adinanta, wanda ta dade da yin watsi da shi, kuma kashi 1 cikin dari na kudin shigarta kawai yake samarwa.

Nijeriya tana da ma'adinai da suka hada da zinare da da kwal da bakin-karfe da gorar-ruwa da baryte da lead da bitumen da sauransu.

TRT Afrika