Nijeriya ta samu sama da dala biliyan 831 daga bangaren man fetur da iskar gas daga tsakanin shekarar 1999 zuwa 2023, a cewar hukumar da ke sa ido kan yadda ake kashe kudaɗen da ake samu daga ma'adinan kasa a Nijeriya (NEITI).
Shugaban hukumar NEITI, Ogbonnaya Orji ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake gabatar da rahoton hukumar na tsawon shekaru 16, wanda aka tattaro da ya shafi kamfanoni 78 a masana'antar ma'adinai ta ƙasar ga kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Gwamnati.
Shugaban ya ce, Nijeriya na buƙatar akalla dala biliyan 20 a duk shekara har zuwa shekaru 10 masu zuwa domin bunƙasa sashen ayyukan iskar gas na ƙasar.
Orji ya kuma bayyana illar da satar danyen mai ta haifar wa ƙasar, inda ya ce Nijeriya ta yi asarar ganga miliyan 701.48 tun daga shekarar 2009, tun daga lokacin da NEITI ta fara bin diddigin asarar da ƙasar ke tafkawa a fannin.
A bangaren gudunmawar da haƙar ma'adinan ƙasa ke samarwa, shugaban na NEITI ya ce an samu kudaɗen shiga da suka kai Naira triliyan 1.56 a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
Duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi a bangaren, shugaban ya ce har yanzu gudunmawar sashen ga kudaden shigar Nijeriya yana kasa da kashi 1 cikin 100.
Hukumar NEITI ta bayyana jihar Ogun da Kogi da Cross River da kuma babban birnin tarayyar ƙasar Abuja a matsayin jihohin da ke kan gaba wajen gudanar da ayyukan ma’adanai da suka samar wa Nijeriya kudaɗen shiga a shekarar 2021.
Domin haɓaka hanyoyin samar da ci gaban, hukumar ta yi kira da a sake nazari kan dokar ma’adanai don sauƙaƙa ayyukan sashen kamar yadda aka kafa dokar masana’antar man fetur (PIA) don ta magance ƙalubale a bangaren mai da iskar gas.