Nijeriya tana fama da matsalar rashin tsayayyiyar lantarki wadda ke tilasta wa gidaje da kamfanoni amfani da janareta. / Hoto: Reuters

Tsarin samar da wutar lantarki a Nijeriya ya kuma samun tasgaro sakamakon 'gazawar tsarin' samar da wutar a safiyar Asabar ɗin nan. Wannan ya janyo birane da garuruwa sun kasance cikin duhu.

Kamfanonin samar da lantarki da dama sun tabbatar wa kwastomominsu cewa an samu gazawar babban layin samar da lantarki na ƙasar, wanda wannan ne karo na uku a mako guda, cewar jaridun ƙasar.

"A halin yanzu muna aiki tare da takwarorinmu don ganin an gaggauta maido da babban layin wuta," cewar kamfanin samar da lantarki na Eko electricity distribution company da ke kudu masu yammacin ƙasar, a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

Hanyoyin wutar lantarki a Nijeriya, wadda ke da tattalin arziƙi mafi girma a Afirka, yana yawan samun matsaloli, kuma hakan yana tilasta wa gidaje da kamfanoni amfani da janareta.

Sashen samar da wutar lantarki na ƙasar yana fuskantar tarin ƙalubale, ciki har da gazawar babban layin wuta, da ƙarancin gas, da bashin kuɗin wuta, da kuma lalata kayayyakin samar da wuta.

Ƙasar tana da ƙarfin iya samar da lantarki na megawatt 12,500, amma tana iya samar da kusan kwatan adadin ne kacal, wanda ya janyo al'ummar ƙasar suke dogaro kan janareta wanda ke da tsadar amfani.

A watan Afrilu, gwamnati Nijeriya ta ƙara kuɗn wuta kan manyan kwastomomi da kashi 230 cikin ɗari.

TRT Afrika