Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar garaɓasar zaftare haraji don bunƙasa juba jarin 'yan ƙasashen waje a fannonin mai da iskar gas na ƙasar.
An sanar da wannan garaɓasa biyu a wata sanarwa da Ministan Kuɗin Nijeriya, Wale Edun ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar da daraktan watsa labarai a hulɗa da jama'a na Ma'aikatar Kuɗi Mohammed Manga ya sanya wa hannu ta ce garaɓasar za ta sa a farfaɗo da fannin kasuwancin mai da gas a Nijeriya.
Sanarwar ta kuma ce daga yanzu kayayyakin sarrafawa da sayar da man dizel, iskar gas, da tsukakken gas, ababen hawa masu aiki da lantarki da kayan girgi masu amfani da makamashi mara gurɓata muhalli da aka shigo da su daga ƙasashen waje ba sa buƙatar biyan haraji.
Manga ya ce wannan ƙoƙari zai haɓaka zuba jari a Nijeriya a fannonin mai da gas, sannan ya haɓaka samar da makamashi, da hanzarta komawa amfani da makamashi mai tsafta.
Wannan umarni na zuwa ne a lokacin da kamfanonin Exxonmobil da Seplat suka gabatar da sabbin tsare-tsare na zuba jari, waɗanda Shugaba Bola Tinubu ya ce nan da wani ɗan lokaci za su samu amincewa daga ma'aikatun gwamnati.
"Wannan kamar yadda Ministan Kuɗi da Haɓakar Tattalin Arziki, Wale Edun ya kaddamar a yau, babban yunƙuri ne na samar da garaɓasa guda biyu na da nufin farfaɗo da sashen mai da iskar gas na Nijeriya: Dokar Sauya Harajin VAT ta 2024 da Sanarwar Janye Haraji ga masu samar da albarkatun mai da gas, kamar yadda dokar ta tanada," in ji sanarwar.
Da yake ƙarin haske, Manga ya ce "Dokar Sauya Fasalin Haraji ta 2024 ta janye haraji daga manyan kayan da suka shafi makamashi, ciki har da dizel, man gas na girki, Gas Ɗin Fetur, Tsukakken Gas, ababen hawa masu aiki da lantarki, da kayan girki masu tsafta."
"Waɗannan matakai za su rage tsadar rayuwa, za su haɓaka samar da makamashi tare da hanzarta komawa amfani da makamashi mai tsafta," a cewarsa.
Ma'aikatar ta kuma ce wannan garaɓasa ta janye haraji na bayyana irin ƙoƙarin da gwamnati take yi na haɓaka cigaba mai ɗorewa, haɓaka samar a makamashi, da cigaban tattalin arzikin dukkan 'yan Nijeriya.
An bayyana cewar wannan mataki zai sa Nijeriya ta zama kan gaba a kasuwar mai da gas ta duniya.