Nijeriya ta amince da cinikin sayar da kadarorin ExxonMobil na dala biliyan 1.28 / Hoto: AP

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta amince da yarjejeniyar cinikin kamfanin Seplat Energy na sayen kadarorinta na cikin teku wa kamfanin mai na Exxon waɗanda darajarsu ta kai dala biliyan 1.28.

Babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NUPRC), Gbenga Komolafe ne ya tabbatar da wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka a ranar Litinin.

''An amince da yarjejeniyar a hukumance'' kamar yadda Mr. Komolafe ya fada yayin jawabinsa a wajen taron bikin cika shekaru 3 da kafa hukumar NUPRC a Abuja.

Matakin dai ya biyo bayan shekara biyu da aka sanar da yarjejeniyar cinikayyar a cikin watan Fabrairu na 2022, wanda ya nuna irin jinkirin da aka samu.

A ranar 1 ga watan Oktoba Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa za a sanar da amincewar cinikin a cikin kwanaki da ke tafe, bayan hukumar NUPRC ta gama aikin tantance tsarin.

Ana sa ran kamfanin Seplat Energy zai mallaki kashi 40 cikin 100 na hannun jari na kadarorin hakar mai guda hudu bayan amincewar da ya samu.

Kazalika kamfanin zai samu wasu muhimman ababen more rayuwa, waɗanda suka haɗa da tashar fitar da kayayyaki ta Qua Iboe da kuma kashi 51 cikin 100 na hannun jari a masana’antar sarrafa iskar gas ta kogin Bonny, wadanda a baya duka mallakin kamfanin mai na Exxon Mobil na gwamnatin Nijeriya ne.

TRT Afrika