China ta yi alkawarin ƙarfafa zuba jari a Nijeriya / Hoto: Shafin fadar shugaban Nijeriya

Nijeriya da China sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da raya albarkatun ɗan' adam da kuma makamashin nukiliya a ganawar da shugabannin ƙasashen biyu suka yi gabannin soma babban taron haɗin gwiwar China da Afirka a ranar Laraba, a cewar mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya.

China, ita ce ƙasa mafi girma wadda ke baiwa Nijeriya lamuni, inda a ƙarshen watan Maris bashin da take bin ƙasar ya kai dala biliyan 5, kamar yadda alƙaluman ofishin kula da basussuka a Nijeriya suka bayyana.

Ƙasashen biyu dai, sun kwashe tsawon shekara 50 suna hulɗar diflomasiyya, sannan sun ɗaɗa karfafa ɗangantakarsu a shekarar 2018 bayan haɗin gwiwarsu a shirin kasuwanci na Belt and Road initiative.

Haɗin gwiwar dai, ta samar da manyan ayyukan more rayuwa a Nijeriya tun daga tashar ruwa mai zurfi zuwa ga layin dogo.

"Akwai buƙatar wannan gagarumin haɗin gwiwar ta samar da ingantacciyar ci gaba da daidaito da kuma tsaro a yankin na Yammacin Afirka, '' in ji Shugaba Tinubu a ranar Talata.

Shugaba Tinubu na daga cikin shugabannin kasashen Afirka 50 da suka isa birnin Beijing a wannan makon domin halartar babban taron haɗin gwiwar China da Afirka na shekarar 2024 wanda shugaba ƙasar Xi Jinping ya kira a matsayin wata dama ta ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin China da Afirka.

"China da Nijeriya, a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, suna karfafa haɗin gwiwarsu a manyan tsare-tsare, waɗanda za su taimaka wajen kara kaimi a dangantakar dake tsakanin China da Afirka da kuma buɗe hanyoyin samar da ci gaba a tsakanin kasashen duniya." in ji shugaba Xi

kasashen biyu sun amince su inganta haɗin gwiwa a fannin hada-hadar kuɗi kamar musayar kuɗin ƙasashen biyu don inganta harkokin cinikayya a tsakani, kamar yadda kamfanin dillancin labaran China ta rawaito shugaba Xi ya ce.

Har ilau sun amince su haɗa kai a kan bayanan sirri don yaki da safarar kuɗaɗe da ba da tallafi ga 'yan ta'adda.

A yayin ziyarar dai, shugaba Tinubu ya samu damar zuwa ɗakin bincike na kamfanin Huawei inda aka yi mishi alƙawarin samar da dakin gwaje-gwaje na kasken rana na haɗin gwiwa a Nijeriya

Kazalika, wani kamfanin China ya yi alƙawarin kafa cibiyar haɗa motoci masu amfani da wutar lantarki da kuma horar da 'yan NIjeriya fasahar kere-kere da bunkasa makamashin da ake sabunta su.

TRT World