Nahiyar Crypto: Tasowar masu aiki da blockchain a Afirka

Afirka za ta zama babbar cibiyar crypto da sarrafa blockchain a nan gaba, a lokacin da sabbin masu kirkirar sa suke wanzuwa don taimakawa yankin wajen magance manyan matsalolinsa. A lokacin da fasahar blockchain ke shirin zama babbar mahadar kudaden yanar gizo a duniya, yanki daya da bai samu cikakkiyar damar amfana da wannan fasaha ba shi ne Afirka.

Amma wannan abu ya fara sauyawa a shekaru biyu da suka gabata, blockchain ya bayyana tare da yaduwa a sashen hada-hadar kudaden yanar gizo na Afirka, kusan a dukkan nahiyar aka rungumi tsarin.

“Afirka na habaka da samun martaba a matsayin cibiya ko matattarar fasahar kasuwancin crypto”, Gideon Greaves, Manajan Daraktan da kamfanin Crypto Valley Venture Capital ya shaidawa TRT World.

“Fara habaka blockchain na yanzu na bunkasa”

Fasahar kirkirar kudaden yanar gizo na crypto sun bayar da damarmaki na karara, hana kaka-gida da magance damfara. Kudaden crypto da ake gina su a kan blockchain, sun ja hankali sosai- amma ba su ne kadai abubuwan dake kan blcochain ba.

A yau, Afirka ce nahiya ta uku a duniya dake habaka da sauri wajen kasuwancin kudin crypto a duniya, inda a hankali take samun zuba jari da yawa. A tsakanin watan Yulin 2020 da Yunin 2021, an rungumi kudin crypto a Afirka da sama da kaso 1,200.

Dan kasuwar dake karbar Crypto a Yammacin Afirka. Gamayyar hauhawar farashi, rashin samun bankuna ingantattu da yawan kusadden da ake biya ya janyo an amince da crypto a Afirka.

Amincewa da rungumar wannan kasuwanci ya fi yawa a kasashe irin su Kenya, Afirka ta Kudu, Tanzaniya da Najeriya, inda rashin mallakar aiyukan gudanar da kudi ta habaka mallakar crypto inda ya zama hanyar da aka zaba a yanzu don aika da kudade. A watan Afrilu, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyata mayar da Bitcoin kudin da za a dinga amfani a shi a kasar, wadda ita ce kasa ta biyu a duniya da ta yi hakan bayan El Salvador.

A wani rahoto da CV VC suka buga a makon da ya gabata mai taken “Rahoton Blockchain a Afirka”, inda aiyukan sarrafa blockchain a nahiyar suka kai dala biliyan 91 a watanni uku na farkon 2022, wanda ya ninku sau kaso 1,668, inda kudaden da ake samu suka karu da kaso 149 a watanni uku na farkon shekarar 2021.

A shekarar 2021 an samu dala miliyan 127, wanda yake kaso 0.5 kudaden daukar nauyin aiyukan blockchaain a duniya. Kaso 96 na wadannan kudade an kashe ne a Najeriya, Kenya, Afirka ta Kudu da Seychelles. Daga cikin wadannan kudade, Fintech business sun zuba dala miliyan 67 (kaso 53) na dukkan kudaden da aka kashe kan blockchain, inda musaya kuma ta kama kan dala miliyan 34 (kaso 26).

Ya zuwa yanzu, tsarin da aka karbe shi gaba daya ya samu tagomashi a watanni 3 na farkon 2022. Kamfanin ‘Pan African crypto exchange’ (MARA) ya samar da dala miliyan 23 a watan da ya gabata; Jambo, kamfanin samar da manhajoji na kasar Kongo ya samudala miliyan 30; Afriex, kamfanin samar da kudaden yanar gizo a Najeriya ya samu dala miliyan 10.

Kamfanin VALR na chanjin kudade a Afirka ta Kudu ya zo kusa da “mega-deal” mai sarrafa blockchain inda a watan Maris sun samu dala miliyan 50, wanda shi ne mafi yawan samar da kudade a nahiyar.

A lokacin da har yanzu ba a samu blockchain ko crypto da yake na dukkan nahiyar ba, amma nan da shekaru biyu zuwa uku za su bayyana. Amma kuma kamfanunnukan fasaha da dama sun kaddamar da blockchain a kasuwancinsu, daga ciki har da kamfanin interswitch na biyan kudade dake Najeriya da kuma FinTech na kasar Sanagal.

“Karin kamfanunnukan kasashen Afirka na shiga sahun kudin gamayya a duniya, kuma muna tsammanin wadannan kudade da dama za su zama kwandalolin blockchain” inji Greaves, wanda ya yi imani da cewa yankin zai jagoranci duniya wajen kasuwancin sarrafa blockchain kain karshen wannan zangon na shekaru goma.

Wani kamfanin mai suna Adanian Labs, da aka samar a 2020 wanda yake da rassa a dukkan Afirka, na horarwa da rainon kananan kamfanunnuka da masu kasuwanci a Afirka da manufar magance matsalolin nahiyar da dama. Manufarsa ita ce rainon kamfanunnukan fasaha 300 a Afirka nan da 2025, inda za a sarrafa blockchain tare da samar da aiyuka ga mutane miliyan daya.

“Game da batun zubi da yanayin kudade, bayanan fayyace mutum, ajje bayanai da rashin samun damar ‘yancin kudade, yanayi da halin da Arirka ta shiga a yau ya janyo wanzuwar sharuddan dake habaka karbuwar fasahar blockchain.”, inji Greaves.

Ya ce, “Wannan ne ya sanya fasahar Afirka ke habaka sosai”. Ya kara da cewa “Yana warware matsalolin dake mutane a kowacce rana a duniya”.

Kirkirar sabbin abubuwa ya zama wajibi

Yawaita da yaduwar wayoyin hannu a Afirka ya sanya nahiyar rungumar hanyoyin biyan kudade na yanar gizo gadan-gadan, kudaden crypto, wadanda ke baiwa mutane damar samun kudade a tsarin da ba a iya juya shi a hukumance, sun zama wani tubalin tattalin arziki sabo.

Tare da ‘yan Afirka miliyan 370 da ba sa mu’amala da banki, wani bangare da kasuwancin blockchain zai yi fice shi ne shigar da kowa da kowa sha’anin kudade. Kasuwannnin Bitcoin na P2P kamar su Paxpul da Localbitcoins ne a kan gaba, suna baiwa miliyoyin mutane damar ta’ammali da kudade.

Shugaba kuma Jagoran Horaswa a Paxpull, Renata Rodrigues ta shaidawa TRT World cewa “Shigar da mutana harkokin ta’ammali da kudade na da muhimmanci wajen nasarar tattalin arzikin kasashe, amma a kasuwanni masu tasowa kamar Afirka, mutane da dama ba sa samun damar ta’ammali da hukumomin kudi.”

“Yawaitar aminta da wayoyin hannu, gami da cigaban fasaha a Afirka ga jama’a, ya sanya nahiyar zama mai shirin kasancewa babbar cibiyar fasaha kamar a ce Bitcoin. Tare da matsalolin kasuwannin kudade na duniya, yawan kudaden da ake kashe da rashin samun damar ta’ammali da banki, karin mutane na ta neman mafitar mu’amalar kudade kamar dai yadda aka rungumi Bitcoin.”

Rodriguees ta bayyana yadda kamfanin wayar hannu na Kenya M-Pesa ya samu nasarar shiga kasashen Afirka inda suke habaka yadda kowa zai yi ta’ammmali da kudade ta yanar gizowa musamman wajen saye da sayarwa. Babban Bankin Kenya (CBK) ya bayyana cewa, ta’ammali da kudade ta yanar gizo a kasar ya karu da kaso 32 a 2021.

“Tare da sani da fahimtar Bitcoin, da kuma yadda ake amfani da shi a nahiyar, za mu samu matsawa ga cigaba sosai, a bar tsarin amfani da kudi na yanzu”.

Hanyoyin chanjin kudaden crypto da dama sun bayyana a ‘yan shekarun nan, kamar ‘pan-African exchange Yellow Card’, wanda a kasashe da dama na Afirka yana aiki, kuma yana shirin fadaduwa zuwa wasu kasashen a nan gaba.

Duba da yadda aiyukan noma suke da muhimmanci a nahiyar, ba abun mamaki ba ne manoma su kalli saka blockchain a bangaren domin warware matsaloli a bangaren. Wani misali shi ne samar da “BeefLedger SA, wanda yake aikida blockchain wajen tantance ingancin naman dabbobin da ake yankawa d ama kayayyakin da ake samarwa da naman domin magance almundahana a kasuwannin Afirka ta Kudu.

Masu taka rawa a bangaren hakar ma’adanai sun yi amfani da blockchain don ganin sun samar da kayayyakin amfaninsu ta hanya mai kyau. A 2018, kamfanin hakar Lu’u-lu’u na Afirka ‘De Beers’ ya kaddamar da Tracr, manhaja ta farko ta blockchain a duniya da aka sadaukar da ita don sanya idanu da tantance sahihancin lu’u-lu’u a kasuwanni.

Greaves na da ra’ayin cewa kasashen Afirka sun shirya don amfana da damarmakin da blockchain ke samarwa a fannoni daban-daban- saboda akwai bukatar hakan.

“’Yan Afirka da dama ba za su iya dogaro kan tsarin mu’amala na kaka-gida da yake da ka’idodi ba. Sun gaji da samun matsaloli a inda ake gudanar da irin wannan tsari. A saboda haka sai sabon tsari ya samu tabarraki wanda zai taimaka wajen habaka mu’amalolinsu”.

Wannan ya kuma haifar da yanayin da ya kawo blockchain tare d habakar kudaden crypto, inji Greaves. Ya ce “A duk inda aka kawo sabbin abubuwai kudade za su samu”.

Daga Suwizalan zuwa Afirka

Wani kamfanin Suwizalan da ya mayar da hankali kan kasuwancin blockchain, CV VC yana shirin tallafawa kananan kamfanunnukan blockchain na Afirka su 100 a shekara mai zuwa da kudi har dala miliyan 50.

Tuni kudin suka fara isa ga gwamman masu kasuwancin blockchain, daga cikin akwai HouseAfrica, wani kamfanin Najeriya dake rajistar yanar gizo kan sha’anin blockchain, da kamfanin Gana na FinTech mai suna Mazzuma, dandali ne na wayar hannu da yake amfani da blockchain da manhaja mai koyatr da kanta donbaiwa jama’a damar biyan kudade a tsakaninsu.

A yanzu haka reshen CV VC a Afirka yana aiki da masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnatoci, cibiyoyin ilimi da bincike da kamfanunnuka don amfani da blockchain wajen warware matsalolin zamantakewa da na tattalin arziki da dama.

Musamman ma ofishin jakadancin Suwizalan a Afirka ta Kudu ya zama mai muhimmanci wajen tabbatar da an yi wannan gamayya da hadin kai tare da samar da tsarin kasuwanci na baidaya ga marasa karfi a kasuwannin Afirka.

Kamfanin Crypto Valley Venture Capital (CV VC) ya bayyana wanzuwar blockchain din Afirka inda aka ware kudi har dala biliyan 10 zuwa 50, a wajen Taron Tattalin Arziki na Duniya a Davos a watan da ya gabata. (Sandali Handagama/CoinDesk).

CV VC dake aiki a Crypto Valley, daya daga cikin cibiyoyin blockchain na duniya (Dake da kwandaloli 14), na shirin inganta bayyana irin kwarewarsa ga Afirka ta yadda za a hade aiyukan masu tasowa na nahiyar a wajen guda bisa doron doka.

A tare da yin hakan, kamfanin na Suwizalan zai fahimci me Afirka za ta bayar na sakamakon bayan amfana da wannan kudi. “Juriya da kokarin Afirka na samun mafita mai inganci abun koyi ne,” inji Greaves.Ya kara da cewa “Yadda aka tafiyar da al’amura daga tsakiya a kasashen da suka ci gaba ba zai kawo mafitar da ake bukata ba ga wannan sabon abu dake girmamam da sauri”.

Greaves ya kuma ce “Kasuwanni na habaka da sauri, babu kamar a Afirka,” ind aya kuma kara da cewa “rashin samar da tsari a baya ne ya bayar da damar watsi da tsohon tsari tare da rungumar kirkirar sabo”.

Greaves na da ra’ayin cewa irin wannan “tsarin da bai shafi gwamnati ba”, hakan ya sanya Afirka zama kan gaba wajen mikawa duniya zuba jari a blockchain, wabu ne sauran kasashen wajen nahiyar za su iya amfani da hakan a masana’antu da kasuwanni.

Fagen Dokoki

A lokacin da ake da kyakkyawan fata ga aminta da fasahar blockchain a bangarori daban-daban, amma akwai wani kalubale.

Babban ciki shi ne matsalar yanar gizo: Yaduwar yanar gizo a Afirka ya tsaya ga kaso 43, inda tsarin amfani da shi a gida kuma yake kasa da kaso 1. Hasashen Bankin Duniya ya bayyana Afirka na bukatar dala biliyan 100 don tafiyar da wannan gibi a cikin sama da shekaru 10.

Sannan akwai kalubalen dokoki, wadanda suke kirkikirar shinge ga adadain mutanen da suke shiga harkokin crypto da kuma amfani da kudaden yanar gizo.

Daga cikin kasashe 54, kasashe 31 sun hana kasuwancin crypto, inda 17 kuma suna da dokoki na rashin tabbas game da crypto, inda 6 ne kadai suke da dokokin da suka halasta kasuwancin.

Afirka ta Kudu, gidan daya daga cikin kasuwancin kudade mafi inganci a nahiyar, ta zama mai sanya dokoki ga harkokin blockchain. Ta samar da dokokin kula da halascin kasuwancin crypto da yin sa ba tareda almundahana ba, inda Babban Bankin kasar ya samar da kudaden yanar gizo har guda biyu.

Dama tuni wata cibiyar hada-hadar kudi ta duniya,Murishiyos ce kasa ta farko da suka rungumi kudin crypto ta hanyar samar da dokoki inda suka samar da kwandalar (ITOs). Seychelles ta dan dauki mataki mai sako-sako wajen yin dokokin da suka shafi crypto kuma suna da daya daga cikin kudaden crypto mafiya karbuwa a aduniya wato (ICOs).

Haka kuma, Kenya ce a duniya a kan gaba kan adadin masu amfani da biyan kudade ta hanyar P2P, ma’ana mutum ga mutum, kuma ta biyar a duniya wajen aminta da crypto. Gwamnatin Kenya ba ta haramta kasuwancin kudin crypto ba, kuma a lokacin da ba a yi musu dokoki ba, Babban Bankin Kenya na lura da tsoma baki a wasu abubuwan da suka shafi crypto.

A kasashe irin su Nigeria, kasuwar crypto na habala sosai duk da haramcin da gwamnati ta kawo (wanda ya karya gwiwar mutane da hukumomi daga amfani da kasuwanci da kudin crypto), inda karyewar Naira ta hadu da biyan kudade ga kasashen waje da yawa, ya sanya neman mafita ga ta’ammuli ga kudade. Najeriya ta zama kasa ta farko a Afirka da ta samar da Ofis Din Chanjin Kudadenta, kudin yanar gizo na e-Naira a watan Oktoban bara.

Duk da rashin tabbas din yin dokoki, kamfanunnuka sun ci gaba da kafa kawunansu tare da bawa jama’a mafita da blockchcin. CV VC ya bayyana kamfanunnuka 41 da suka samu tallafi daga Janairun 2021 zuwa Marsi din 2022 inda suka shigar da blockchain a masana’antu da dama.

Greaves ya bayyana cewa “Kasashen dake kan gama kamar su Afirka ta Kudu da Murishiyos sun nuna mataki na cigaba game da kudaden crypto da yadda za su amfanar. Irin wannan kafa doka ake bukata wanda ya zaburara da waus sun biyo baya”.

“A lokacin da aka samu dokokin baidaya da aka amince da su, za a samu karin damarmaki sosai.”

TRT World