Wani dan kwadago yana jiran dako a wata kasuwa da ke Colombo, a Sri Lanka, ranar Lahadi, 26 ga Yuni, 2022. Hoto: AP Archiv / Photo: AP Archive

Wata hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi ministocin kudi na kasashen duniya da zau dan daga kafa ga kasashe matalauta da ake bi tarin basussuka, tana kiyasta cewa annobar Covid-19 da hauhawar farashi da ake fama da ita da kuma tarin basussukan da ake bi sun sanya karin mutum miliyan 165 cikin talauci.

Hukumar ta Shirye-Shiryen Ci gaba ta MDD ta ce karuwar na nufin fiye da kashi 20 na al'ummar duniya - kusan mutum biliyan 1.65 a yanzu suna rayuwa kan kasa da dala 3.65 a rana da kuma fafutukar neman abin da za su ci.

Taron da Ministocin Kudi na Kungiyar G20 za su yi a Indiya a mako mai zuwa zai tattauna ne kan dakile talauci, da sauya fasalin manyan hukumomin kasa da kasa da kuma tsarin basussukan da ake bin kasashe.

Rukunin na ministocin kudi na kasashe 20 da za su yi taro a Indiya sati mai zuwa, za su tattauna kan shawo kan talauci, tare da sauya fasalin cibiyoyin kudi na kasa da kasa da fitar da jadawalin bashi na duniya.

Achim Steiner, Jagoran UNDP, ya bayyana matakin talaucin da ake da shi yanzu a matsayin mai tsoratarwa.

Ya fada wa 'yan jarida cewa, "Wannan yana nufin duk gwamnatin da ba za ta iya biyan malamanta ba; da gwamnatin da ba za ta iya daukar likitoci da nas a asibiti ba, da samar da magani da cibiyoyin lafiya a karkara".

Hukumar UNDP ta ce Duka sauran mutum miliyan 165 da ke talauci suna rayuwa ne a kasashe masu karanci ko matsakaicin samun kudi.

Matakin talauci yana raguwa kadan-kadan har zuwa farkon annobar COvid-19, amma a yanzu ya kar hawa.

Bashi ya yi wa kasashe masy karancin arziki kanta

Tashin kudin ruwa yana nufin kasashe mafi talauci a yanzu suna kashe ninki biyu ko uku na kason kudin da suke samu, wajen biyan bashi, idan aka kwatanta da kasashe masu arziki.

Kasashe matalauta suna kashe karin kusan ninki 2.3 kan kudin ruwa, sama da ayyukan tallafawa jama'a.

Steiner ya ce UNDP ta yi kira don samar da "Tsayar da Bashi da talauci", don kasashen da ke fuskantar matsanantan matsaloli su iya amfani da arzikinsu kan samar da ababen saukaka rayuwar jama'arsu.

Wannan zai yi daidai da shirin nan na baya, wanda ake kira Shirin Dakatar da Biyan Bashi, wato (DSSI), wanda kungiyar G20 ta yi, don taimakon kasashen matalauta a lokacin Covid-19.

Hukumar UNDP ta yi kiyasin kasashe 25 masu karancin arziki suna kashe sama da kashi 20 cikin dari na kudaden da suke samu kan biyan bashi a shekarar da ta gabata.

Wannan adadin shi ne mafi girma tun 2000, kuma zai iya tashi matukar kudin ruwa ya ci gaba da tashi a duniya.

Steiner ya kara da cewa, "Musamman ga kasashe masu karancin samun kudi, shawo kan nauyin bashi ya zamo abu mara dorewa".

Kira don neman gyara harkar kudi a duniya

Kawar da talauci daya ne daga cikin muradun cigaban na MDD, inda take kokarin shawo kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke shan kan duniya zuwa shekarar 2030.

Babban Sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira da kawo manya-manyan sauye-sauye a tsarin hada-hadar kudi na duniya, don ba da dama samar da tsarin adalci wajen rabon arzikin duniya.

Wani rahoto na wannan satin ya nuna kusan kashi 30 na dala tiriliyan $92 na bashin gwamnati a duniya, na kasashen masu tasowa ne.

Steiner ya jaddad cewa, "Muna bukatar sabon tsari don gano matsalolin da shawo kansu," kuma ya kara da cewa dakile mummunan tasirin da aka samu kan kasashe matalauta, zai sa a kashe dala biliyan $107, ko kashi 0.065 na GDP din duniya".

Reuters