Arzikin Nijeriya da Masar dai sun ragu sakamakon fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudadensu./ Hoto: AFP

Hasashen tattalin arzikin duniya na IMF ya ƙitasta dala biliyan 253 a matsayin kudaɗen shigar Nijeriya na cikin gida bisa ga farashin dala a bana, inda kasar Aljeriya mai arzikin makamashi take da dala biliyan 267, sai kuma Masar wadda take da dala biliyan 348 da Afirka ta Kudu da ke da dala biliyan 373.

Tattalin arzikin Nijeriya wanda ya kasance mafi girma a nahiyar Afirka a shekarar 2022, na shirin komawa zuwa matsayi na huɗu a bana, a cewar hasashen Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF.

Kazalika hasashen ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Masar da ke kan gaba a shekarar 2023 zai koma matsayi na biyu bayan Afirka ta Kudu, sakamakon raguwar darajar kudi da aka samu.

Afirka ta Kudu wacce ta fi kowace ƙasa ƙarfin masana'antu a nahiyar Afirka, za ta ci gaba da zama a matsayin kafin Masar ta sake karɓewa a shekarar 2027.

Ana kuma sa ran Nijeriya za ta ci gaba da zama a matsayin na hudu har tsawon shekaru masu zuwa, a cewar alkaluman rahoton hasashen IMF.

Arzikin Nijeriya da Masar ya ragu sakamakon fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudadensu.

TRT Afrika