Kamfanin Dangote ya ce yana fatan kamfanin mai na Nijeriya NNPC zai sake kawo ƙarin ɗanyen fetur ɗin a wannan watan da ma wani daga kamfanin ExxonMobil. 

Sabuwar matatar mai ta Dangote ta Nijeriya ta karɓi ganga miliyan ɗaya ta ɗanyen man fetur daga kamfanin Shell, wanda hakan ya zamo karo na biyu da matatar ta karɓi mai a cikin wannan watan, yayin da take shirye-shiryen fara ayyukanta, in ji mai magana da yawun kamfanin a ranar Laraba.

Matatar man dai ba ta fara aiki a kan lokaci kamar yadda aka tsara ba, amma ana sa ran fara aikin nata a yanzu zai mayar da ƙasar, wacce ta fi kowacce samar da mai a Afirka zuwa babbar mai fitar da tattacen fetur, wani buri da ƙasar ta daɗe tana son cimma.

Mai magana da yawun matatar fetur ta Dangote ya ƙi faɗar daga inda aka kawo ɗanyen fetur ɗin, amma ya ce a ranar Larabar nan za a sauke ɗanyen fetur ɗin a wajen matatar da ke Legas.

Kamfanin Dangote ya ce yana fatan kamfanin mai na Nijeriya NNPC zai sake kawo ƙarin ɗanyen fetur ɗin a wannan watan da ma wani daga kamfanin ExxonMobil.

Ƙungiyar OPEC ta sanya wa Nijeriya ta fitar da adadin fetur har ganga miliyan 1.5 a baɗi, amma gwamnatin ƙasar ta ce tana shirin samar da ganga miliyan 1.8 don tabbatar da wadatar da masana'antar Dangote da matatun mai mallakin gwamnati da ake yi.

Reuters