Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da ingancin kayayyaki da sinadaran da matatar mansa ta ke amfani wajen samar da man dizal a Nijeriya.
Dangote ya tabbatar da haka ne a yayin ziyarar da kwamitin da ke sa ido kan ayyukan man fetur a majalisar wakilan Nijeriya ya kai matatar man a ranar Asabar karkashin jagorancin shugaban majalisar Hon. Tajudeen Abbas.
''Shugaban majalisar ya bayyana damuwarsa game da ce-ce-ku-cen da ya mamaye zargin rashin ingancin kayayyakin da ake shiga da su Nijeriya da kuma shirin kwamitin majalisar na gudanar da sahihin bincike kan batun,'' a cewar wata sanarwa da sashen yada labarai na kamfanin Dangote ya fitar a ranar Lahadi.
''Za a gudanar da sahihin bincike tare da gwajin kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da man matatar Dangote da kuma wadanda ake shigowa su, in ji Hon. Tajuddeen,'' a cewar sanawar.
Sanarwar kamfanin ta karyata zargin da shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya ''Midstream da Downstream,'' Farouk Ahmed wanda a kwanakin baya-bayan nan ya bayyana cewa man dizal da ake shigowa da su ƙasar ya wuce wanda kamfanin dangote ke samarwa a cikin gida tare da zargin cewa yana ɗauke da sinarin sulfur.
Ahmed dai ya zargi matatar man Dangote da wasu matatun mai kamar Waltersmith da Aradel da samar da man dizal da ke ɗauke da sinadarin sulfur da yawan shi ya 650 zuwa 1200- lamarin da ya janyo suka daga 'yan Nijeriya da dama waɗanda ke ganin hanya ce ta fifita kayayyakin da ake shigowa da daga ƙasashen waje.
Kazalika Ahmed ya zargi mamatar wadda ta shafe watannin tana sayar da man dizal ga kamfanonin jiragen sama a Nijeriya, da cewa har yanzu ba ta da lasisi, yana mai cewa har yanzu tana matakin soma aiki ne.
Tuni dai hukumar ta buƙaci kwamitin majalisar wakilai a Nijeriya da ya gaggauta samar da sahihin rahoto bisa binciken tabbatar da ainihin sinadarin da matatar Dangote ta ke amfani da shi wajen samar da man dizal da kuma yawan shi.