Manoma a Ghana sun ɗora alhakin tsananin ƙaranci da hauhawar farashin kayan lambu kan ayyukan masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.
Masu haƙar ma'adinan wadanda ake kiransu da 'Galamsey' a harshen cikin gida na Ghana, wato ''tara su a sayar,'' an fi saninsu da gudanar da ƙananan harkokin haƙo ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, musamman zinari a fadin ƙasar.
Baban sakataren ƙungiyar ma'aikatan noma (GAWU) Edward Kareweh, a ranar Alhamis ya bayyana cewa ayyukan 'yan galamsey sun mamaye mafi yawan gonakin kayan lambu a fadin ƙasar, lamarin da ke janyo tsaiko ga manoma wajen samun wuraren da za su gudanar da ayyukansu, a cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Ghana GNA.
Ya kuma kara da cewa ayyukan 'yan galamsey sun haifar da zaizayar kasa tare da gurbata ruwa amfani da kuma lalata kasa, inda ya yi gargadin cewa lamarin zai yi muni, da dai sauransu yana mai gargadi kan cewa yanayin na iya tsanani idan ba a dauki matakan da suka dace ba.
Hauhawar farashin ƙananan 'yan kasuwa
''Kayan lambu amfanin gona ne da ke buƙatar kulawa sosai, kamar ruwa mai tsafta wajen yin shuka, amma ba lallai ba ne a buƙaci ruwa mai tsafta wajen shuka koko ko kuma kwakwar manja don ruwan da za a zuba a ƙarƙashinsa ba lallai ne ya zama ruwa da mutum zai sha,'' in ji Kareweh.
Farashin ƙananan 'yan kasuwa na kowane kilogiram din kayan lambu a kudin Ghana Cedi a birnin Accra da Kumasi zuwa watan Yunin 2024 yana kai wa tsakanin GHS 10.56 da GHS 21.12, a cewar Hukumar Kididdigar Ghana.
Akwai tazara mai yawa idan aka kwatanta da 12.5 GHS kan kowane kilogram da ake sayar da kayan lambu a watan Janairun shekarar nan.
Kazalika Kareweh ya jaddada cewa sauran abubuwan da suka taimaka wajen tsadar kayan lambun sun hada da share gonaki domin shirin yin noma da kuma magungunan kashe ƙwari, wadanda ke da matukar muhimmanci ga samar da kayan lambu da kuma taƙaita illa ga ɓangaren noma na Ghana.