Kotun Kolin Nijeriya ta yarda a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira

Kotun Kolin Nijeriya ta yarda a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira

Kotun Kolin Nijeriya ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira a kasar.
Tun a watan Nuwamban shekarar 2022 ne gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gabatar da sabbin takardun kudin kasar. / Hoto: Fadar Shugaban Nijeriya / Hoto: Reuters  

Kotun Kolin Nijeriya ta yanke hukuncin a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin Naira a kasar har sai baba ta gani.

Hukuncin ya biyo bayan zaman kotun mai mambobi bakwai a ranar Laraba, inda aka ba da umarnin a ci gaba da karbar tsofaffi da sabbin takardun Naira a kasar a matsayin halastattun kudade na cinikayya da kasuwanci a hukumance.

A baya dai an sanya ranar 31 ga Disamba na 2023 a matsayin wa'adin daina amfani da tsofaffin kudaden.

Idan za a iya tunawa, a watan Maris ne kotun ta janye dokar hana amfani da tsofaffin takardun kudi a kasar, tana mai ba da umarni a ci gaba da gudanar da hada-hada da takardun kudin har zuwa karshen shekarar 2023.

Kotun ta kafa hujjar cewa gwamnati ta gaza bai wa ‘yan kasar isasshen lokaci domin musayar tsofaffin takardun kudin.

Dakile zamba da almundahanar kudade

A watan Nuwambar 2022 ne tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta bullo da sabbin takardun kudin na Naira da manufar daile ayyukan zamba da almundahana a kasar.

Takardun kudin Naira da aka sabbunta sun hada da Naira 200 da 500 da kuma 1,000.

TRT Afrika