Kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya ya ƙaru da kashi 115.5 daga Lira tiriliyan 1.85 (dala biliyan 79.4) a 2023, kamar yadda rahoton Ma'aikatar Kasuwanci ya bayyana.
Yawan saye da sayarwar da aka samu ya ƙaru da kashi 22.3 inda a shekara ake samun ƙarin biliyan 5.87, in ji rahoton da mai taken 'Nazari kan Kasuwanci ta Hanyar Intanet a Turkiyya' da aka fitar a ranar Litinin.
Ana hasashen kuɗaɗen da za a samu zai kai dala biliyan 109.4 a wannan shekarar kuma adadin saye da sayarwa zai kai biliyan 6.67.
A 'yan shekarun nan yawaitar kasuwanci ta hanyar intanet ya daɗu sosai, daga kashi 10.1 a 2019 zuwa kashi 20.3 a 2023.
Adadin gudunmawar da kasuwanci ta intanet ke bayarwa ga kuɗaɗen shigar ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 33.3 a shekara bayan shekara inda ya ƙarkare kan kashi 6.8 a 2023.
A yayin da kayayyaki da kayan amfani a cikin gida ƙanana ne suka mamaye kasuwancin intanet a Turkiyya da suka samar da dala biliyan $10, sai kayan lantarki na dala biliyan 5.8. inda tufafi, takalma da kayan gyara su suka kama na dala biliyan 5.41.