Kamfanin Jiragen Sama na Emirate mallakin Hadaddiyar Daular Larabawa ya sauka a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Talata, bayan kusan shekaru biyu da ya dakatar da ayyukansa saboda tangardar diplomasiyya da kasa kwashe kudadensa daga kasar.
Jirgin mai lamba EK 783 ya sauka a filin jiragen sama na MMIA da misalin karfe 3:32 na ranar Talata, inda rahotanni suka ce babu mutane da yawa a cikin jirgin samfurin Boeing 777.
Ba a gudanar da wani bikin saukar jirgin ba da tankar ruwa ko shewa, sakamakon samun labarin gidanar da zanga-zanga a Nijeriya da kamfanin ya samu.
Jirgin zai dinga jigilar fasinjoji a kowace rana tsakanin Dubai da Legas.
A makon da ya gabata Nijeirya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun amince kan yarjejeniyar sauke hakkokin juna, inda Emirate zai dinga zuwa Nijeriya, haka shi ma jirgin kamfanin Air Peace zai dinga zuwa DUbai yana dawo wa Legas.
Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Festus Keyamo, tare da mahukuntan susurin jiragen sama na HDL sun amince kan sabuwar yarjejeniyar Huldar Jiragen Sama (BASA) tsakanin kasashen biyu.
An rawaito ministan na cewa "Tattaunawar mai muhimmanci ta samar da yarjejeniyar sauke hakkokin juna, tare da tabbatar da cewa jiragen saman Nijeriya ma za su samu damar fara tashi kai tsaye zuwa HDL. Wannan cigaba ne mai tarihin gaske ga sashe sufurin jiragen saman Nijeriya, inda matafiya suka samu damar fadada zirga-zirga zuwa kasashen waje."
A matsayin na babbar cibiyar kasuwanci a Afirka, Nijeriya ta kulla kakkarfar alakar cude ni in cude ka da Hadaddiyar Daular Larabawa tsawon shekaru.
Haka zalika baya ga jirgin fasinja, bangaren jigilar kaya na Emirates Skycargo ma zai taka rawa wajen habaka kasuwanci zuwa Nijeriya da fita da kaya daga kasar zuwa waje.
Kamfanin ya ce zai tallafa wa kasuwancin Nijeriya ta hanyar fitar da kayayyakin kasar zuwa DUbai, daga nan kuma zuwa kasashen Malaysia, Hong Kong, Bahrain da sauran su.
Kamfanin zai kuma dinga shigo da waus kayyaki zuwa Nijeriya daga manyan kasuwanin HDL, India da Hong Kong.