Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Emirates ya sanar da cewa zai ci gaba da tashi daga Nijeriya daga ranar 1 ga Oktoban wannan shekara.
Emirate ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, inda ya ce daga nan zai dinga tashi kowace rana tsakanin tsakanin birnin Legas na Nijeriya da Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Mataimakin kamfanin na Emirates Adnan Kazim ya ce "Muna farin cikin dawo da tashin jiragenmu zuwa Nijariya."
"Bisa al'ada hanyar Lagos-Dubai ta yi fice a wajen abokan hulɗarmu a Nijeriya," a cewar Adnan.
Ya kara da cewa "Muna godewa gwamnatin Nijeriya saboda haɗin kai da taimako wajen sake farfaɗo da wannan hanya, sannan muna fatan yin maraba da fasinjojinmu."
A watan Agustan 2022 ne, kamfanin na Emirates ya dakatar da safara daga Nijeriya, saboda saɓani da gwamnatin ƙasar wajen fitar da kuɗaɗen kamfanin na cinikin da yake yi daga Nijeriya.
Gwamnnatin Nijeriya ta yi marhabin da matakin na Emirates, inda ta ce dama ta daɗe tana jiran wannan rana.
"Kamfanin Emirates yi babbar sanarwar a hukumance wacce muke jira, Emirates zai ci dawo Nijeriya a wajen Oktoba," a cewar Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya Festus Keyamo a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.