Nijeriya na cikin manyan ƙasashen duniya da suke da arzikin man fetur. / Hoto: Reuters / Photo: AP

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar da rahoton da ke nuna yadda farashin man fetur ya tashi daga watan Afrilu zuwa watan Mayun da ya gabata.

Ƙididdigar hukumar ta bayyana cewa matsakaicin farashin man fetur ya tashi da ninkin kashi 223% cikin 100 a faɗan ƙasar, inda a watan Mayun 2024 aka sayar da lita man kan Naira ₦770. A watan Mayun 2023 dai an sayar da man kan ₦238.11.

Rahotan ya ce ƙaruwar farashin mai daga wata zuwa wata ya kai kashi 9.75% cikin 100, inda a watan Afrilun da ya gabata aka sayar da man kan ₦701.24 duk lita guda, yayin da a watan Mayu ya koma ₦770.

A jihar Jigawa da ke Arewa maso yammacin ƙasar ne aka fi samun tsadar farashin mai, inda ya kai ₦937.50 duk lita. Sai jihohin da suke biye da ita, wato jihar Ondo inda farashin ya kai ₦882.67, da jihar Benue inda ya kai ₦882.22 duk lita.

Su kuwa jihohin Legas da Naija da Kwara su ke da mafi ƙarancin farashin man inda aka sayar da shi kan ₦636.80 a Legas, sai ₦642.16 a Naija, sai kuma ₦645.15 a Kwara.

Idan aka duba yankunan Nijeriya kuwa daban-daban kuwa, rahoton ya nuna cewa yankin Arewa masu Yamma shi ne ya fi samun tsadar mai, inda matsakaicin farashi ya kai ₦845.26.

Jihohi uku da farashin ya fi ko ina tsada a watan Mayun da ya gabata su ne, Adamawa (₦1709.00), da Sokoto (₦1675.00) da kuma Bauchi (₦1657.92).

Shi kuwa yankin Arewa ta tsakiya shi ne yankin da ya fi kowanne sauƙin man, inda matsakaicin farashi ya kai ₦695.04.

TRT Afrika