Ana yawan samun katsewar wutar lantarki a Ghana saboda ƙarancin wutar lantarki amma abin ya kara kamari a 'yan kwanakin nan. / Hoto: Getty Images

Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF ya buƙaci gwamnatin Ghana ta inganta tsarin tafiyar da harkokin makamashin ƙasar domin magance ƙalubalen rashin samar da wutar lantarki da ake yawan fama da ita a kasar a baya-bayan nan.

A kwanan nan ne Ministan Kudi na Ghana Dokta Mohammed Amin Adam ya bayyana cewa ''ɓangaren makamashin ƙasar na da giɓin kuɗi na kusan dalar Amurka biliyan 1.9.''

Tuni dai Minsitan ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su saka hannun jari a ɓangaren makamashi, inda ya jaddada cewa gwamnati ta kafa sashin ne domin samun riba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana (GNA) ya rawaito.

''An samu ci gaba wajen ƙara fayyace gaskiya da kuma shawo kan wasu matsaloli da ake fama da su, ciki har da aiwatar da tsarin kuɗin fito, sai dai akwai buƙatar a ƙara ƙaimi wajen inganta harkokin shugabanci da rage hasarar fasaha da kasuwanci,'' in ji IMF.

Asusun IMF ya bayyana cewa ɓangaren makamashi yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Ghana, inda ''matsalar wutar lantarki a halin yanzu ke shafar rayuwar mutane da dama,'' a cewar wata wasiƙa da IMF ya aika wa GNA.

IMF ya jaddada muhimmanci inganta tsarin tafiyar da harkokin makamashi, musamman la'akari da magance hasarar da fasaha da kuma kasuwanci.

Ta ce a ƙarƙashin shirinta na Bayar da Bashin dala biliyan uku ga Ghana, Asusun, tare da Bankin Duniya suna taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da sauye-sauye a ɓagaren.

"Waɗannan sauye-sauyen za su ɗauki lokaci, sannan mun yi ƙudurin ci gaba da aiki tare gwamnati don taimakawa wajen gina ɓangaren makamashi mai dorewa domin Ghana ta gobe." a cewar kakakin asusun.

TRT Afrika