A Nijeriya, hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a watan Fabrairu, saɓanin kashi 29.90% da aka gani a Janairu, a cewar bayanan da suka fito ranar Juma'a daga cibiyar ƙididdiga ta ƙasar, Nigeria’s Bureau of Statistics (NBS).
Sanarwar ta ce, "Duba da sauyin, hauhawar farashi a Fabrairun 2024 ya nuna ƙaruwar maki kashi 1.80%, idan an kwatanta da Janairun 2024".
Bayanan sun nuna cewa a ma'aunin shekara bi-da-bi, hauhawar farashi a Nijeriya ya kasance da ƙarin kashi 9.79%, idan an kwatanta da kashi 21.91% da aka samu a Fabrairun 2023.
NBS ta ce, “Wannan na nuna cewa hauhawar farashin a matakin shekara bi-da-bi ya ƙaru a Fabrairun 2024, idan aka kwatanta da irin wannan watan a shekarar da ta gabata (wato, Fabrairun 2023)”.
Haka nan kuma, hauhawar farashin kayan abinci a Fabrairu ya kasance 37.92% a matakin shekara bi-da-bi.
Wannan ya kasance da ƙarin kashi 13.57% idan an kwatanta da yadda aka gani a Fabrairun 2023 (24.35%), a cewar rahoton.
Tun a baya, ƙaruwar tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. Sai dai kuma, gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa za ta magance waɗannan matsaloli.