Kayan marmari na daga cikin abubuwan da ake saye a kullum lokacin azumi kuma yawanci masu sayarwa sun fi son kudi hannu/Photo AA

Ofishin Mataimakin Shugaban Nijeriya tare da hadin gwiwar Bankin Masana’antu (Bol) ya ce za a fara bayar da lamuni na Naira biliyan 75 ga masu ƙananan sana’o’i da ƙanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs) a watan Janairun 2024.

Mista Temitola Adekunle-Johnson, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan samar da ayyukan yi da kula da ƙanana da matsakaitan masana’antu na ofishin mataimakin shugaban kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Talata.

Adekunle-Johnson ya ce matakin wani kokari ne na cika alkawarin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na goyon bayan sauye-sauyen da ake samarwa a fannin kula da ƙanana da matsakaitan masana’antu da ake yi a kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN ya rawaito.

Ya bayyana cewa rancen, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 75 za a bai wa kananan ‘yan kasuwa a fadin kasar a kan kudin ruwa na kashi tara cikin 100.

Adekunle-Johnson ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya da Bankin Masana'antu za su yi amfani da hanyoyin da ake da su wajen samar da rancen ga kananan ‘yan kasuwa, inda ake son mayar da hankali kan mata da matasa.

Ya ce gwamnatin Tinubu tun bayan hawansa mulki ta hada kai da masu ruwa da tsaki a sassan gwamnati da masu zaman kansu domin ba da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a fannin tallafi da lamuni.

Adekunle-Johnson ya ce: “Kwanan nan, hukumar gudanarwar Bankin Access ta amince da sake duba shirinta na ba da lamuni ga masu ƙaramin ƙarfi daga Naira biliyan 30 zuwa Naira biliyan 50.

"Nazarin da aka sake yi, a cewar bankin, shi ne ƙara yawan masu cin gajiyar shirin lamuni na bankin da kuma yin tasiri ga rayuwa".

TRT Afrika da abokan hulda