Orano ne ya mallaki kashi 63.4 na lasisi a kamfanin Somair da ke haƙar ma'adinai a Nijar, yayin da gwamnatin Nijar take da kashi 36.6. / Photo: AFP

Kamfanin makamashin nukiliyar Faransa Orano ranar Laraba ya ce hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun ƙwace ikon "gudanar" da tasharsa ta makamashin yuraniyom da ke ƙasar ta Yammacin Afirka.

Da ma dai a watan Oktoba ne kamfanin na Orano ya sanar da dakatar aiki a tasharsa da ke Nijar sakamakon abin da ta bayyana a matsayin ƙarin matsin lamba da yake fuskanta daga hukumomin ƙasar a fannin gudanarwa da harkokin kuɗi.

Orano ne ya mallaki kashi 63.4 na lasisi a kamfanin Somair da ke haƙar ma'adinai a Nijar, yayin da gwamnatin Nijar take da kashi 36.6.

"Kamfanin Orano ya kwashe watanni da dama yana gargaɗi game da katsalandan ɗin da yake fuskanta wajen tafiyar da harkoki a Somair," in ji wata sanarwa da kamfanin na Faransa ya fitar.

"Ba a aiwatar da matakan da kamfanin ya amince da su a wurin taron manyan shugabanninsa, don haka, a yau, Orano yana tabbatar da cewa hukumomin Nijar sun karɓe ikon gudanar da Somair," in ji sanarwar.

A watan Yuni, hukumomin Nijar sun soke yarjejeniyar da aka ƙulla da Orano domin haƙo yuraniyom a mahaƙar ma'adinai ta Imouraren, wacce ke da nauyin aƙalla tan 200,000.

Gwamnatin sojin Nijar, wadda ta hau kan mulki a watan Yulin da ya gabata, ta ce za ta sabunta dokokin haƙar ma'adinai na ƙasar.

AFP