COPEC ta yi hasashen samun ragin kashi 4 cikin 100 na farashin man fetur daga 16 ga Satumba a Ghana

Ƙungiyar Masu Amfani da Man Fetur a Ghana (COPEC) ta yi hasashen samun ragi a farashin man fetur daga a ranar Litinin,16 ga watan Satumban 2024 a ƙasar.

COPEC ta ce za a samu matsaƙaicin ragin kashi 4 cikin 100 a farashin man fetur da dizal da kuma iskar gas a Ghana, a wani mataki na samarwa masu saye da amfani sassauci a yanayin da ake ciki na rashin tabbas a farashin man fetur a duniya.

''Sai dai, idan an samu wani gagarumin sauyi wanda ba a shirya masa ba a farashin man fetur da ake samu daga ƙasar da ke samar da man a duniya'' kamar yadda babban Sakataren ƙungiyar COPEC, Duncan Amoah ya bayyana.

Ya ƙara da cewa, ''kasuwa ta nuna cewa za a samu ragi a farashin dillalan man fetur da dizal da kuma gas a Ghana, yanayin da zai amfanar da masu sayen kayan a farashin ciniki na gaba da zai kankama daga ranar 16 ga watan Satumba.''

Hasashen COPEC ya yi nuni da cewa matsakaicin farashin man ferue zai ragu zuwa kuɗin Ghana cedi 12.959 kan kowace lita, yayin da dizal da gas za su ragu zuwa cedi 13.642 kan kowace lita sai kuma cedi 15.345 a kowane kilogram na gas.

An dai danganta wannan ragi da ake hasashen samu da saukin farashin man fetur a kasuwannin duniya, inda matakin farashin danyen mai ya yi ƙasa sosai a bana.

COPEC ta kuma buƙaci gwamnati da aiwatar da tsauraran matakai da za su tabbatar da rage haraji kan kayayyakin man fetur, musamman gas, don inganta hanyoyin samu da kuma amfaninsa.

Kazalika hakan zai taimaka wajen hana sare dazuzzuka da yawan illar amfani da itace.

Haka kuma, ƙungiyar ta COPEC ta ba da shawara kan a farfaɗo da matatar mai ta Tema (TOR) don rage yawan dogaro da ake yi kan albarkatun mai da ake shigowa da su Ghana tare da hana gurbatacecen mai shiga ƙasar.

TRT Afrika