Sai dai farashin na bitcoin a ‘yan makonnin nan ya tsaya inda yake a ƙasa da dala 100,000 a daidai lokacin da ‘yan kasuwa ke neman masu saye. / Hoto: Reuters

Darajar kuɗin kirifto na Bitcoin ta kai dala 100,000 a karon farko bayan zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ɗaukar matakai na barin kasuwa ta yi halinta da tsame hannu a harkar kirifto idan ya kama aiki a wata mai zuwa.

Kuɗin na kirifto ya kai dala 100,000 a safiyar Alhamis, inda ya yi ta hawa sama tun bayan da Trump ya lashe zaɓe a farkon watan Nuwamba, wanda ya sha alwashin mayar da Amurka “babban birnin bitcoin da yin kirifto a duniya”.

Kuɗin na kirifto ya ƙaru da fiye da kaso 50 tun bayan da fitaccen mai kuɗin ya samu nasara a zaɓen – haka kuma kuɗin ya ƙaru da kusan kaso 134 tun bayan da aka shiga shekarar.

Sai dai farashin na bitcoin a ‘yan makonnin nan ya tsaya inda yake a ƙasa da dala 100,000 a daidai lokacin da ‘yan kasuwa ke neman masu saye.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ya zaɓi ɗaya daga cikin shahararrun ‘yan kirifto Paul Atkins domin zama shugaban hukumar kula da hada-hadar hannayen jari.

Atkins wanda ya kasance kwamishina a hukumar tun daga 2002 zuwa 2008, ya ƙirƙiro kamfanin tuntuɓa na Patomak Global Partners a 2009, inda waɗanda yake wa aiki suka haɗa da bankuna da masu cinikayya da kamfanonin kirifto.

Wata sanarwa da gwamnatin mai jiran gado ta Trump ta fitar ta bayyana cewa Atkins ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin sashen cinikayya ta intanet waɗanda ke amfani da kadarori na intanet tun daga 2017.

TRT World