Kasar Afirka ta Yamma na fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru, inda kudin cedi ya yi rauni sosai da kuma hauhawar farashi. Hoto: REUTERS

Ci-gaban tattalin arzikin Ghana ya ragu zuwa kashi 2.0 cikin 100 duk shekara a rubu'i na uku na shekarar 2023 daga kashi 3.2% a rubu'in da ya gabata, sakamakon koma bayan da aka samu a fannin masana'antu, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta sanar a ranar Laraba.

Kasar Afirka ta Yamma na fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru, inda kudin cedi ya yi rauni sosai da kuma hauhawar farashi.

Hukumar kididdigar ta ce abin da yake ba da gudunmawar koma bayan da aka samu a rubu'i na uku na shekarar shi ne matrsalar da masana'antu ke fuskanta kamar hakar ma'adinai da gine-gine.

Sai dai harkar noma ta ba da gudunmawa mai kyau, duk da cewa noman koko yana da mummunan yanayi.

A halin yanzu hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa 2.0% a cikin Nuwamba daga kashi 9.7% da aka samu a watan Oktoba, ofishin kididdiga ya fada a wani jawabin daban a ranar Laraba.

Haka kuma hauhawar farashin kayayyakin masarufi ta ragu a watan da ya gabata, zuwa kashi 26.4% daga kashi 35.2% na watan Oktoba.

Ghana na tattaunawa kan yarjejeniyar sake fasalin basussuka tare da masu karbar bashi a hukumance.

Tana fatan cimma yarjejeniya nan ba da jimawa ba don samun dala miliyan 600 na gaba daga asusun lamuni na duniya a karkashin wani shirin ceto na dala biliyan uku.

Reuters